Feb 07, 2016 07:41 UTC
  • Muhimmancin Ilimi Da Tarbiyyar Yara Da Matasa

Muhimmancin Ilimi Da Tarbiyyar Yara A Mahangar Addinin Musulunci

Ilimantarwa da tarbiyya al’amura ne masu girman matsayi da daukaka kuma sune ginshikin rayuwa da suke kai mutum ga kyakkyawar rayuwa da samun cikan kamala. Hakika mutum wani halitta ne da ke bukatar tarbiyya a fagen rayuwarsa kuma sakamakon kyakkyawar tarbiyya  zai iya kai wa ga babban matsayi na tsarkakan ruhi da yalwan ilimi a rayuwarsa ta duniya. Hakika tun daga yarantar mutum har zuwa girmansa da kuma zuwa karshen rayuwarsa yana rayuwa ce a kan matakai masu bibiyar juna kuma a tsawon matakan rayuwarsa yana da damar kai wa ga mataki madaukaki, kamala da cika.
A cikin wannan dan gajeren sabon shirin da zamu gabatar muku na “Yara manyan gobe” zamu yi kokarin bijiro da muhimman hanyoyin tarbiyya ne tun daga matakin yaranta har zuwa samartaka musamman a mahangar addinin Musulunci da fatan masu saurarai zaku kasance tare da mu don jin abin da shirin ya kunsa.


Hakika matakin kula da tarbiyyar yara lamari ne mai muhimmanci da ke bukatar sanya ido da lura, kuma dole ne a kan mahaifa ko masu kula da tarbiyyar yara su kasance masu cikakken sa- ido kan tarbiyyar yaran da lura da dabi’unsu. A fili yake cewa tarbiyya da ilimantarwa al’amura ne masu muhimmanci da daukaka a rayuwar mutum musamman daga lokacin yaranta zuwa lokacin samartaka, kuma wadannan matakai biyu na yaranta da samartaka suna kunshe da tarin matsaloli na musamman, sakamakon haka tarbiyya da ilimantarwa suna da matakai, kuma kowane mataki yana da nashi matsayi da muhimmanci na musamman.
Tarbiyya a ma’anarta ta lugga tana nufin karuwa, girma da habaka a kan tafarkin da ake bukata, ko kan tafarki mai kima. Yayin da neman ilimi hanya ce da take kai mutum ga samun tarbiyya da kyakkyawan sakamakon rayuwa. Don haka a fili yake cewa neman ilimi da samun tarbiyya sune shimfida kuma ginshikai da suke kai ga inganta rayuwar bil-Adama tare da taimaka masa wajen cimma burin rayuwarsa na kai wa ga matsayin cika da kamala da ake bukata.


Hakika duk wata halitta da take kan doron kasa tana da kebantacciyar hanyarta ta kai wa ga cikan halitta da aka kebe mata, kuma wannan ita ce manufar samar da ita a fagen rayuwa. Don haka manufar neman ilimi da tarbiyya a rayuwar mutum ita ce kokarin samun saukin kai wa ga cikan halitta da daukaka da aka kaddara masa a fagen rayuwa, kuma mutum yana matsayin khalifan Allah ne a kan doron kasa.
Allah Madaukaki a cikin Suratul-Baqara a aya ta 30 yana fayyace mana cewa: “Kuma a lokacin da Ubangijinka ya ce ga Mala’iku; hakika Ni mai sanya wani wakili ne a kan bayan kasa, sai suka ce; Shin zaka sanya wanda zai yi barna a kanta kuma ya zubar da jini alhalin mu muna maka tasbihi da godiya tare da tsarkake ka, sai {Allah} ya ce lallai Ni na san abin da ba ku sani ba”. Hakika dan Adam ba kawai halitta ba ne da zai iya zama mai tarbiyya, a’a halitta ne da yake bukatar samun ilimi da tarbiyya. Tabbas bukatar dan Adam ga ilimi da tarbiyya a rayuwa; bukata ce mai girma, kuma da zarar ya rasa wannan albarka a rayuwarsa, to tabbas ya yi hasarar babbar dama mai kima da take matsayin fitila mai haskaka hanya gare shi.


Sakamakon haka duk mutumin da ya rasa ilimi da tarbiyya a rayuwarsa, to babu makawa zai zame ya rasa gishirin zaman rayuwar duniya kuma rayuwarsa zata zame ta dogara da sauran mutane. Immanuel Kant masanin ilimin falsafa dan kasar Jamus da ya rayu a karni na goma sha takwas yana da imanin cewa: “Batun ilimi da tarbiyya al’amura ne biyu masu girman muhimmanci a rayuwa, kuma sune mafiya matsala da suke addabar mutum a fagen rayuwa”. Har ila yau Kant yana da akidar cewa: “Daga cikin kirkirar mutum akwai samar da daula da tsarin gudanarwa da kuma tsarin neman ilimi da tarbiyya, amma wadannan abubuwa sun fi zama matsala a gare shi a kan saura al’amura”.
A bisa dabi’ar duk wani mutum kafin girmansa, dole ne sai ya kai ga wasu matakai masu muhimmanci a rayuwarsa na cikan hankali da kamala. A yau sabon ilimi da ake kira da “Ilimin halayyar dan Adam mai zurfi” yana dauke da bangarori daban daban misalin ilimin sanin girman jiki, zamantakewa, sanin halayya, ruhi da dabi’a, jin kai, harshe da sauransu.


A mahangar masana ilimin halayyar dan Adam, matakin tarbiyya yana fara wa ne tun daga lokacin da aka haifi jariri, kuma haka tarbiyyar zata ci gaba a matakan rayuwar dan Adam daban daban. A misali Jean Piaget masanin ilimin halayyar dan Adam dan kasar Faransa yana cewa: Bunkasar ilimin mutum ta rabu zuwa matakai hudu ne, kuma ta kan zo karshe ne da zarar mutum ya cika shekaru goma sha shida a duniya. Shi ma Erik Erikson masanin ilimin halayyar dan Adam dan kasar Amurka yana cewa: “Fadada da zurfin hankalin mutum da ke rayuwa a tsakanin al’umma tun daga haihuwarsa har zuwa karshen rayuwarsa ya rabu zuwa mataki takwas ne”. A takaice dai masana ilimin halayyar dan Adam sun kasa matakan tarbiyyar mutum zuwa matakai takwas kamar haka:-


{1} Kafin haihuwar mutum wato tun daga lokacin farkon samuwarsa a cikin mahaifa a lokacin da yake maniyi a cikin mahaifiyarsa har zuwa lokacin haihuwarsa.
{2} Lokacin da yake jariri har zuwa cikan shekaru shida.
{3} Lokacin yaranta daga shekaru shida zuwa shekaru goma sha biyu.
{4} Matashi daga shekaru goma sha biyu zuwa shekaru ashirin.
{5} Samarta daga shekaru ashirin zuwa talatin.
{6} Tsaka-tsakar shekaru daga talatin zuwa shekara hamsin.
{7} Matakin cikan hankali daga shekaru hamsin zuwa shekaru sittin da biyar.
{8} Tsufar mutum daga shekara sittin da biyar zuwa sama.


Har ila yau masana ilimin zamantakewa sun yin maganganu masu muhimmanci dangane da tarbiyar dan Adam. A bisa mahangar masana ilimin zamantakewa: Tarbiyya hanya ce da ta gare ta al’umma zasu kai ga inganta lafiyar jikinsu da na ruhinsu, kuma har su kai ga yin tasiri ga al’ummun da zasu zo a bayansu. A fili yake cewa kowace al’umma tana kokarin ganin duk wadanda zasu zo a bayanta sun dauki irin salon tarbiyya da tunanin da ta tafi a kai. Sannan iyalai suna daga cikin tushen tarbiyya a tsakaninal’umma. Haka nan mafi yawan manazarta suna bada muhimmanci ga tushen tarbiyya a tsakanin iyali misali mahaifa musamman ma mahaifiya.