Apr 27, 2016 16:12 UTC
  • Tarbiyyan Jariri Bayan Haihuwarsa {3}

Masu saurare barkanku da warhaka, kuma barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na “Yara manyan gobe”. A shirye-shiryenmu da suka gabata mun gabatar muku da wasu daga cikin matakan tarbiyyar jariri ne bayan haihuwarsa, tare da bayani kan muhimmancin nonon uwa, sai lokaci yayi mana halinsa don haka a yau zamu dora daga inda muka tsaya kamar haka:-

Masu saurare barkanku da warhaka, kuma barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na “Yara manyan gobe”. A shirye-shiryenmu da suka gabata mun gabatar muku da wasu daga cikin matakan tarbiyyar jariri ne bayan haihuwarsa, inda muka fayyace cewa; Batun tarbiyyar jariri ba lamari ne da ake gudanar da shi a dan gajeren lokaci kuma cikin sauki ba, wato al’amari ne da ake gudanar da shi tsawon lokaci kuma sannu a hankali ta hanyar bin matakan tarbiyya ingantattu. Sannan muka gabatar muku da wasu daga cikin ladubba masu muhimmanci da ake gudanarwa ga jariri bayan haihuwarsa tare da tasirinsu a fagen tarbiyya da rayuwar yara.

Idan za a tuna a shirinmu da ya gabata muna bayani ne kan muhimmancin nonon uwa da irin girman tasirinsa a fagen tarbiyyar jiki da na ruhin jariri, sai lokaci ya yi mana halinsa don haka zamu ci gaba daga inda muka tsaya, sai a biyo mu domin jin abin da shirin ya kunsa:-

Hakika bayan gagarumin tasirin nonon uwa a fagen tarbiyyar jiki da na ruhin jariri, sannan matakin da mahaifiya zata dauka wajen jiyar da jaririnta karatun alkur’ani mai girma da ambaton Allah Madaukaki gami da addu’o’i a lokacin shayarwa, hakan yana gagarumin tasiri a fagen dora yaro a kan tafarkin shiriya. Sakamakon haka sai mahaifiya ta zame ta karfafa jiki da tunani gami da ruhin jaririnta a lokaci guda. Kan haka malaman tarbiyyar Musulunci suke bayyana cewa: Idan har yaro ya kasance yana sauraren karatun alkur’ani da addu’o’i, to babu mamaki ya kai ga babban matakin tarbiyya a rayuwarsa.

Dangane da gagarumin tasirin nonon uwa da muhimmancinsa a fagen tarbiyyar yara tare da kasancewarsa abinci mafi muhimmanci da soyuwa ga jarirai, alkur’ani mai girma ya ambaci batun shayar da nonon a wajaje goma sha daya misali a cikin Suratul-Baqara aya ta 233 Allah Madaukaki yana fayyace muhimmancin nonon uwa da cewa: “Kuma iyaye {mata} suna shãyar da ‘ya’yayensu ne shẽkara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shãyarwa”.

Hakika a cikin wannan aya mai tsarki an fayyace tsawon lokacin shayar da jariri nonon mahaifiya, don haka zamu iya kai ga sakamakon cewa tsawon lokacin shayar da jariri nonon mahaifiya shekaru biyu ne cur, inda jariri yake da hakkin amfana da nonon uwarsa a tsawon wannan lokacin saboda nonon mahaifiya shi ne abinci mafi dacewa kuma garkuwa ga jariri daga kamuwa da wasu nau’in cututtuka.

Duk da cewa a cikin ayar an fayyace cewa mahaifa suna da damar raba yaronsu da nonon mahaifiya kafin cikan shekaru biyu amma wasu ruwayoyi sun kaiyade adadin wannan lokacin da watanni uku, wato mahaifa zasu iya raba jaririnsu da nonon mahaifiya bayan cikan watanni ashirin da daya. Haka nan batun uzuri da lalura ta lafiya da ke tilasta raba jariri da nonon mahaifiya a kowane lokaci musamman bullar matsalar jiki da na ruhi da ta shafi uwa ko jariri kafin cikan shekaru biyu.

Har ila yau duk da cewa a lokacin da mahaifiya ke shayar da jaririnta nono tana jin aminci da yardar zuci kan gagarumin jin kai da hidimar da take gudanarwa a fagen renon jaririnta amma duk da haka shari’a bata tilasta mata shayar da jaririn ba, kuma tana da damar karbar ladar kudi daga mahaifin jaririn kan shayar masa da dansa. Hakika shari’ar Musulunci ta fayyace hukunce-hukunce gami da hakkoki dangane da rayuwar mahaifiya da jaririnta tare da kiyaye adalci a karkashin tsarin iyali.

Tabbas sakamakon muhimmancin nonon mahaifiya da irin gagarumin tasirinsa kan yara; hadisai daga Annabin Rahama Manzon Tsira Muhammadu dan Abdullahi da iyalan gidansa tsarkaka {a.s} sun jaddada muhimmancin daukan matakin shayar da yara wannan nonon. Manzon Allah {s.a.w} yana bayyana cewa: “Babu wani nono da yafi nonon da mahaifiya zata shayar da danta”. Haka nan shugaban muminai Imam Ali dan Abi-Talib {a.s} yana bayyana cewa: “Babu wani nono da za a shayar da yaro da zai kai nonon mahaifiyarsa albarka”. A fili yake cewa; Nonon mahaifiya yana gadar da lafiyar jiki da karfafa ruhin jariri tare da yin gagarumin tasiri a rayuwarsa.

Yana daga cikin muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa; gagarumin tasirin da nonon ke yi a fagen magance matsalar bullar tamowa wato karancin abinci mai gina jiki ga kananan yara, saboda babu wani nau’in abinci da ya fi nonon uwa gina jiki da gadar da lafiya, kamar yadda nonon uwa yake gagarumin tasiri wajen rage mutuwar kananan yara da jarirai gami da magance matsalar cutar numbashi ga yara da sauran cututtuka da suke saurin kama yara tare da wahalar da su. Sakamakon haka hakki ne da ya rataya a wuyar mahaifa a fagen kare lafiyar da rayuwar yaransu su dauki duk matakan da suka dace wajen ganin sun shayar da su nonon uwa.

Kamar yadda shayar da jariri nonon uwa yake da muhimmanci tare da tasiri a fagen tarbiyyar yara, haka nan irin abincin da mai shayarwa zata ci yake da girman muhimmanci, wato dole ne abicin ya kasance tsarkakekke na halal saboda abin da uwa zata ci shi ne ke tasiri wajen samar da nonon da zata shayar da jaririnta. Tabbas idan abincin da mahaifiya take ci, gurbatacce ne da aka nemo ta hanyar haramun, shakka babu wannan abincin zai yi mummunar tasiri a ruhin jaririn da take shayar da shi gami da tarbiyyarsa.

A fege guda kuma a karkashin koyarwa da ladubbar addinin Musulunci a fagen shayar da jariri nono; Abin so ne a lokacin shayar da jariri ko ciyar da yara mahaifiya ko mai shayarwa ta kasance cikin alwala tare da fara shayarwar ko ciyarwa da sunan Allah.

Haka nan yana da kyau a lokacin shayar da jariri nono ya kasance an shayar da shi ta gefen hagun. Kan haka an ruwaito daga Imam Ja’afar Sadiq {a.s} cewa: “Nonon hagun na mahaifiya, shi ne waje mafi dacewa domin shayar da jariri nono”. Haka nan bincike na ilimi ya tabbatar da wannan batu na muhimmancin shayar da jariri nonon uwa ta bangaren hagun tare da gabatar da shawarar yin hakan. Saboda ta gefen hagun ake jin sautin bugun zuciya, kuma jin bugun zuciyar uwa da jariri yake yi yana tsananin yin tasiri a fagen kwantar masa da zuciya.