Apr 27, 2016 15:40 UTC
  • Tarbiyyan Jariri Bayan Haihuwarsa

Masu saurare barkanku da warhaka, kuma barkanmu da sake saduwa da ku a ci gaban shirinmu na “Yara manyan gobe”. A cikin shirinmu na yau zamu fara ambaton wasu daga cikin matakan tarbiyyar jariri ne bayan haihuwarsa, sai a biyo mu don jin abin da shirin ya kunsa:-

A fili yake cewa; Batun tarbiyyar jariri, ba lamari ne da ake gudanar da shi a dan gajeren lokaci ba, hakika al’amari ne da ke daukan tsawon lokaci sannu a hankali tare da bin matakan tarbiyya da suka dace domin dora yaro a kan ingantaccen tubali mai karko. Tabbas tarbiyyar mutum lamari da ke cike da tarin kalubale da matsaloli, don haka ba abu ne mai sauki ba, sakamakon haka komawa ga tafarkin addini da mahangar kwararru kan harkar tarbiyya ya zame dole musamman hadisan da aka ruwaito daga Manzon Tsira, Annabin Rahama Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} da na iyalan gidansa tsarkaka {a.s}. Hakika tsarin rayuwarsu da maganganunsu masu albarka suna cike da kyawawan dabi’u da halayen cika da kamalar dan Adamtaka da zasu gamsar a fagen gudanar da tarbiyyar jariri har zuwa girmansa.

Daya daga cikin ladduba masu muhimmanci bayan haihuwar jariri ita ce yin kiran sallah da iqama a kunnensa. Hakika yana daga cikin kowayarwa addinin Musulunci mai muhimmanci yin kiran sallah da iqama a kunnen jaririn da aka haifa. Tabbas farko matakin da Manzon Rahama Muhammadu dan Abdullahi da iyalan gidan tsarkaka {a.s} suke dauka kan jaririn da aka haifa shi ne gudanar da kiran sallah a kunnensa na dama tare da yin iqama a kunnensa na hagun. Imam Sajjad {a.s} yana bayyana cewa: “A lokacin da aka haifi Imam Husaini {a.s} Manzon Allah {s.a.w} ya gudanar da kiran sallah a kunnensa”. A wasu ruwayoyin kuma an bayyana irin tasirin da kiran sallah da iqama suke da shi a fagen tarbiyya da ruhin jaririn da aka haifa, inda suke fayyace cewa; Kiran sallah da iqama suna gadar da nutsuwa ga ruhin jariri.

Har ila yau yana daga cikin tasirin kiran sallah da iqama a kunnen jariri, gadar masa da tarbiyyar addini da koyar da shi farkon tushen akidar Musulunci da ke kunshe da kadaita Allah da gaskata sakon annabcin Manzon Allah Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w}. Sakamakon haka tun farkon zuwa yaro duniya zai fara ne da sauraren akidar Musulunci a matsayin shimfidar rayuwa, inda a nan gaba zai samu kwanciyar hankali da nutsuwa da dukkanin koyarwar akidar tare da rungumarta a matsayin tafarkin gudanar da rayuwa.

Haka zalika yana daga cikin ladubbar tarbiyya masu muhimmanci sanya kyakkyawar suna ga jaririn da aka haifa. Hakika sanya suna ga duk wani abin da mutum yake gudanar da mu’amala da shi yana da muhimmanci a fagen rayuwa, kamar yadda sanin sunayen abubuwa da suke kewaye da mutum suke da muhimmanci ciki har da abin da ya haifa. Sakamakon haka zabar suna domin radawa jaririn da aka haifa yana da muhimmanci na musamman a fagen rayuwa. Kan haka addinin Musulunci ya jaddada muhimmancin zaba wa jariri sunan da ya dace tare da rada masa kyakkyawa daga cikin sunayen. Shugaban muminai Imam Ali dan Abi Talib {a.s} yana bayyana cewa: “Ku rada wa jariranku suna tun kafin zuwansu duniya…”. Wato ku tantance kyawawan sunayen da zaku sanya wa jariranku tun kafin haihuwarsu. A wasu lokuta saboda rashin sanin hakikanin abin da za a haifa wato namiji ne ko mace, sai mahaifa su dauki matakin tantance kyakkyawar sunan da zasu rada wa jaririnsu a tsakanin sunayen maza da mata.

Hakika babban abin lura kuma abu mafi muhimmanci a fagen rada sunan jaririn da aka haifa shi ne; zabarwa jaririn kyakkyawar suna mai ma’ana. Manzon Tsira Annabin Rahama Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} yana fayyace cewa; Zabar wa jariri kyakkyawar suna yana daga cikin hakkokin yara a kan mahaifansu. Kamar yadda Imam Musa Al-Kazim {a.s} ke bayyana cewa: “Wani mutum ya zo wajen Manzon Allah {s.a.w} ya ce; Mene ne hakkin dana a kai na? Sai Manzon Rahama {s.a.w} ya amsa masa da cewa; Ka sanya masa suna mai kyau, ka tarbiyyantar da shi kyakkyawar tarbiyya, kuma ka shimfida masa hanyar kai wa ga matsayin da ya dace da shi”.

Tabbas Jagororin shiriya na iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka {a.s} suna sanya kyawawan sunaye masu cikar ma’ana ga ‘ya’yayensu tare da yin wasici ga sauran mutane kan sanya wa ‘ya’yayensu kyawawan sunaye masu cikar ma’ana irin ta addini, gami da gargadinsu kan nisantar rada wa ‘ya’yansu munanan sunaye marassa ma’ana. Kan haka shugaban muminai Imam Ali dan Abi-Talib {a.s} ke bayyana cewa; “Farkon kyautatawar mutum a kan dansa shi ne zaba masa kyakkyawar suna”.

Bayan wannan dan takaitaccen bayani kan bukatar sanya kyakkyawar suna ga jaririn da aka haifa, to abin tambaya a nan shi ne; Wani tasiri hakan yake da shi a kan jariri? Hakika kyakkyawar suna tana da gagarumar tasiri a kan jaririn da aka haifa. Abu na farko shi ne; Daga sunan mutum ana iya fayyace hakikanin zurfin tunanin mahaifansa, al’adarsu, matsayinsu da kimarsu a tsakanin al’umma. Sakamakon haka a wasu lokuta; daga sunan mutum jama’a suke zartar da hukunci kan irin ma’amalar da zasu gudanar da shi tare da sauraren irin martanin da zasu ganin daga gare shi.

Haka nan a kowace al’ada da dabi’ar mutane; suna da wasu sunaye ko lakabobi na musamman da suke amfani da su a kan ‘ya’yayensu, kuma irin wadannan sunaye da lakabobi suna da ma’anoni da fassarori na musamman, inda da zarar mutumin da yake da masaniya kan wannan al’adar ya ji wannan sunar, tunaninsa zai tafi zuwa ga irin wadannan ma’anoni da fassarori, kuma idan wannan suna da lakabi suka kasance kyawawa, to a fili yake cewa; suna gadar da daraja da mutumci ga mai dauke da wannan sunar tare da samun girmamawa da kallon mutunci daga sauran mutane. Tabbas sunan mutum tana tasiri wajen fayyace matsayi da darajarsa a idon mutane a tsawon rayuwarsa. Sakamakon haka idan sunar mutum ta samo asali ne daga kyakkyawar siffa da tushe na tarbiyya da dan Adamtaka, to babu shakka wannan siffa da daraja zasu ci gaba da bibiyar mutum a rayuwarsa musamman idan ya zage dantse a fagen ginin ya siffantu da wannan kyakkyawar siffa da sunansa ke kunshe da shi.