Ko Kun San (43) 12-Urdeebehesht-1395 Hijira Kamarian
Yau Lahadi 12-Farvaddeen-1395H.SH=23-Rajab-1437H.K=01-Mayu-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 138 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Rajab-1299H.K. Aya. Sayyeed Husain Kohkamraee daya daga cikin manya manyan malaman addini a zamaninsa ya rasu . Aya. Kohkamraee yana daga cikin daliban Sheikh Murtada Ansaria babbam mar'ja'I na zamaninsa a birnin Najaf na kasar Iraqi. Aya. Sayyed Kohkamraee yana da dalibai fiye da 800 sannan ya wallafa littafai a fannoni daban daban na ilmi. Daga cikin littafan da ya rubuta akwai "Risala-amalia" kan fikihu da ibada.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 127 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Mayu-1889M. Majalisar ma'aikata ta duniya ta tsaida ranar daya ga watan mayu na ko wace shekara a matsayin ranar ma'aikata da dunia. Majalisar ta dauki wannan matsayin ne don a rannan ne a shekara 1886M. Ma'aikata kimani dubu 40 a birnin Chicago na kasar Amurka suka fito zanga zangar neman Karin albashi da kuma hakkokinsu na jin dadin ma'aikata. Amma gwamnatin kasar Amurka ta lokacin ta tura jami'an tsaro na yansanda wadanda suka yi dirar mikiya a kan ma'aikatan, inda da dama daga cikinsu suka rasa rayukansu wasu kuma suka ji rauni. Amma bayan haka gwamnatin ta biya wadansu daga cikin bukatun nasu. Don haka ne majalisar ta tsaida wannan ranar a matsayin ranar ma'aikata ta duniya don tunawa da wancan ranar.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Urdeebehesht-1358H.SH. Ustaz Aya. Murtada Muttahari daya daga cikin fitattun malaman addini wadanda suka jagoranci juyin juya halin musulunci zuwa ga nasara a nan kasar iran yay i shahada. Uztaz Muttahari ya na daga cikin mashawartan Imam Khomaini (q) wanda ya assasa JIM, kafin da kuma bayan samun nasara. Bayan samun nasara ne Imam ya sanyaci cikin majalisar juyin juya halin musulunci kuma shugabanta. Amma watanni ukku kacal bayan samun nasara wani daga cikin yayan wata kungiyar batattu ya kasha shi bayan ya kamala wata zama yana komawa gida shi kadai. Imam Khomaini (q) ya kodaita da wadanda suke son samun wayewar zamani su karanta littafan Shaheed Muttahari wadanda suka kai 80. Ranar shahadar Aya. Muttahari, it ace ranar Malamai a nan Iran.