Ko Kunsan (328) 22 ga watan Bahman shekara ta 1394 Hijira Shamsiyya
Yau Alhamis 22 ga watan Bahman shekara ta 1394 Hijira Kamaria wacce tayi dai dai da 2 ga watan Jamasa-Ula shekarata 1437 Hijira Kamaria, har'ila yau wacce ta yi dai dai da 11 ga watan Febrerun shekara ta 2016 Miladia.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22 ga watan Bahman shekara ta 1357 Hijira Kamaria, mutanen kasar Iran karkashin jagorancin Imam Ruhullah Almusawi alkhomaini sun sami nasarar juyin juya halin musulunci wanda ya kawo karshen mummunan bakin tarikinta da jagorancin azzaluman sarakuna na lokaci mai tsawo. Kafin wannan nasara dai musulman kasar Iran maza da mata da matasa da tsoffi kowa ya yi abinda zai iya don ganin bayan mulkin sarakuna a kasar da kuma. yan sa'aee kafin samun nasarar kusan a ko wani babban gari an yi ta samun rikci tsakanin sojojin wadanda suke son zuwa birnin Tehran don hana shi faduwa hannun masu gwagwarmaya da sarakunan Pahlawi, amma suna rufe titunan suka hana sojojin ficewa daga garuruwansu. Wannan ya tilastwa sojojin bayya matsayinsu na babu ruwammu. Da haka kuma cibiyoyi gwamnati masu muhimmanci, daga cikinsu harda gidajin radio da television suka yi ta fadawa hannun majahidai inda daga karshen aka ji muryoyi suka tashi da Allhu Akbar juyin juya halin musulunci ya kai ga nasara an kawo karshen azzaluman sarakuna kasar Iran kuma musulunci ya aki ganasara karkashin jagorancin Imam Khumaini (q). Muna taya al-ummar iran da kuma dukkan masu son 'yenci a duniya murnar cika shekaru 37 da nasarar juyin juya halin musulunci a Iran.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 26 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Febreru-1990 Miladia shugaban bakaken fata masu gwagwarmaya da tsarin wariyar launin fata a kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela bayan shafe shekaru 27 a tsare ya fito daga kurkukun da ake tsare da shi a kudancin kasar. gwamnatin wariyar launin fata ta Afrika ta kudu ta yanke hukuncin zaman kaso na tsawon rayuwa ne kan Mandela a shekara 1963 Maladia saboda gwagwarmaya da gwamnatin wariyar. Sai kuma a shekara ta 1991 Miladia aka kawo karshen tsarin wariyar launin fata a Afrika ta kudu bayan gwagwarmayan mutanen kasar da kuma takurawa na kasashen duniya kan gwamnatin ta wariya. Sannan a shekara 1994 aka gudanar da zaben shugaban kasa inda Nelson mandela ya zama shugaban 'yentacciyar kasar Afrika ta Kudu bakar fata na farko.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 5 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11 ga watan Febrerun shekara 2011 Miladia, tsohon shugaban kasar Masar wanda ya dauki kansa a matsayin shugaba sai illa-masha'allah ya sauka daga kujerar shugabancin kasar bayan zanga zangar miliyoyin mutanen kasar da kuma zaman nuna rashin amincewarsu da shugabancinsa na kwanaki 18 a dandalin Tahrir na birnin Alkahira. Bayan faduwar gwamnatin Zainul abideena bin Ali a kasar Tunisia wata guguwar farfawar musuunci ya kada a kasashen larabawa wanda ya kai ga kifar da wasu gwamnatoci masu karfi a yankin, wadanda suka hada da na Tunisiar Masar da kuma Libya. Mubarar ya karbi shugabancin kasar Masar ne a shekara 1981 Miladia bayan kissan da aka masu kishin addini cikin sojojin kasar suka yiwa Anwar Sadat saboda ha'inci da ya yiwa mutanen kasar na sulhuntawa da HKI. Husne Mubarak ma ya ci gaba da siyasar da Sadat a duk tsawon shekarun da yake mulkin kasar. Amma bayan da sojojin da Mubarak ya mikawa mulki suka gudanar da zabe aka mikawa Muhammad Mursi na kungiyar ikhwanul Muslimin, kura kuran da ya yi ta yi ya kai ga sojoji suka sake kwace ikon kasar a cikin karamin lokacin . da haka kuma ya batawa mutanen kasar juyin juya halin nasu.