May 02, 2016 04:58 UTC

Yau Laraba 15- Urdeebehesht -1395H.SH=26-Rajab-1437H.K=04-Mayu-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa ranar 15-Urdeebehesht na ko wace shekara a kalandar Iran, ran ace ta girama "Aheikh Assuduq" shahrerren malamin shia  a tarihin musulunci. An haifi sheikh Saduk wato Abu Jaafar Mohammad ibn Babawaih a shekara ta 306 H.K. a birnin Qum na kasar Iran. Bayan kamala karatu a cikin gida. Sheikh Saduq ya fara wasu tafe tafiye na neman ilmi da kuma tattara hadisan manzon All..(s) da iyalan gidansa masu tsaki.  Bayan zagayawa zuwa kasashen daban daban, ya yada zanga a birnin Bagdaza na kasar Iraqi inda malaman suka fa'idantu da ilminsa. Sheikh Saduk ya karbi hadisan manzon All…(s) da iyalan gidansa masu tsarki daga wajen kimanin malamai 200 kuma ya tattarasu a wani littafi mai suna "من لایحضر الفقیه" a cikin mujalladai hudu. Kuma littafin na daga cikin littafan shia sanannu guda hudu mai hadisai 6000. Da kuma wasu  littafai wadanda suka hada da امالی، خِصال، عیون اخبار الرّضا(ع) و عِلَلُ الشرایع.  Sheikh Saduk ya rasu a shekara ta 381H.K. yana dan shekara 75 a duniya.


02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1440 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-Rajab-Shekaru 3 kafin Hijira. Abu Talib (r ) ammin manzon Al…(s) kuma mahaifin Aliyu ya rasu a Makka a dai dai lokacinda suke cikin takunkuman tattalin arzikin da quraishawa suka yiwa musulmi da dangin Bani Hashim. Bayan rasuwar kakan manzon Al..(s) Abdulmuttalib, AbuTalib ne ya rike shit un yana dan shekara 8 a duniya. Abu Talib ya musulunta, ya kuma yi wasiyya ga mutanensa su tallafawa manzon Al..(s) a bayansa. Har'ila yau a ciki kwanakin ne Matar manzon Al..(s) ta Farko Hadiza yar Khuwaila(r ) ta rasu. Don haka ne ma manzon All… (s) ya kira sheakarar rasuwarsu a matsayin shekarar bakin ciki.


03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 73 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Urdeebehesht-1323H.SH. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa JMI, ya gabatar da khudubarsa ta farko kan harkokin siyasa da kuma kirin mutanen Iran musamman malaman addini daga cikinsu zuwa gwagwarmaya, wacce it ace kadai tafarkin fitar da al-ummar musulmi da kuma mutanen Iran daga kangin zaluncin da suke karkashin azzaluman sarakunan da masu goya masu baya daga cikin turawa yan mulkin Mallak. Da wannan jawabin ne Imam Ya bude gwagwarmayansa da azzaluman sarakunan kasar Iran.