May 02, 2016 05:09 UTC

Yau Alhamis 16- Urdeebehesht -1395H.SH=27-Rajab-1437H.K=05-Mayu-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1450 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Rajab-13Kafin Hijira. All..ta'ala ya aiko da manzon Al..(s) Mohammad Dan Abdullahi a matsayin annabi kuma manzo. Manzon Al..(s) yana dan shekara 40 a duniya a lokacinda Mala'ika Jibril (a) ya zu masa da bishara kan cewa shi annabin All..ne manzon zuwa ga dukkan talikai. Kafin Haka manzon Al..(s) yakan je kogon hira a dutsen Noor daga wajen birnin Makka inda yake bautawa Al..ta'ala sannan ya yi tunani a kan halittun All.. Don haka tun lokacin ne aka dora mas nauyin isar da sakon Al.. ga talikai. Ranar aiko da manzon Al…(s) babban rana ce ga dukkan talikai wadanda aka aikowa wannan sakon. Muna taya musulmi da kuma duniya da wannan rana da bushara da sakon Al…na karshe garesu.


02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 198 da suka gabata a rana irin ta yau wato 05-Mayu-1818M. Aka haifi Karl Marx wani baturen kasar Jamus wanda ya kafa iqidar komunisanci a duniya.  Da farko Karl Marx Lawya ne, sannan ya karanci tarihi da kuma ilmin farsafa. Daga nan ne ya fara bayyana ra'ayinsa kan harkokinn siyasa da kuma zamantakewa a duniya . Littafinsa mai suna "Manufesto" shi ne yake kunshe da ikidarsa ta cewa ci gaban dan adama ya dogara ne kan rabun arziki a tsakaninsu. Don haka ne ma yay i has ashen cewa nan gaba a duniya za'a sami ma'aikata wadanda zasu kwace iko daga yan jari hujja su daidaita mutanen duniya gaba daya a cikin arziki.


Don irin wannan akidarsa ne gwamnatin kasar Jamus ta kore shi daga kasar zuwa kasar Ingila inda ya kamala sauran rayuwarsa. Sai dai bayan mutuwarsa akidarsa ta sami karbuwa a wasu kasashen duniya har aka kafi gwamnatin kominisanci mafi girma a duniya a tarayyar Soviet a shekara 1917. Amma bayan shekaru kimani 70 gwamnatin ta fadi, hasashen Kalmax ya zama karya, Kalmax yana da wani littafi mai suna "Jari". Kalmax ya rasu a shekara 1883.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 35 da suka gabata a rana irin ta yau 05-Mayu-1981M. Wani dan rajin gwagwarmayan nemawwa kasar I-landa ta arewa mai Suna Bobby Sands ya mutu a cikin wani korkuku a kasar ta I-landa bayan yajin cin abinci na kwanaki 66. An haifi Bobby Sands a shekara ta 1954M a birnin Belfost babban birnin kasar Iland ta arewa ya tashi ya sami cewa turawan ingila suna mamaye da kasarsa. Don haka ya gudanar da rayuwarsa wajen ganin kasarsa ta sami 'yencin kanta, kuma a kan wannan hanyar aka kama shi aka jefa shi cikin kurkuku inda ya shiga yajin cin abinci na kwanaki 66, kafin y ace ga garinku, ko kuma yam utu. A halin yanzu ana daukar Bobby a matsayin gwarzon kwatar 'yencin ilanda ta arewa.