May 02, 2016 05:13 UTC

Yau Jumma'a 17- Urdeebehesht -1395H.SH=28-Rajab-1437H.K=06-Mayu-2016M

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1377 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Rajab-60H.K. Ayarin Imam Husain (a) tare da iyalansa sun fara tafiya zuwa karbala inda ta farko ta yi zanga a birnin Makka na wasu watanni. Imam Husain ya fita daga birnin Madina ne bayan mutuwar Mu'awiya dan abi sufyan, da kuma hawar mu'awiya kan kujerar sarauta a kasar Sham. Bayan haka ne sarkin ya bukaci Imam Husain(a) yay i masa bai'a. Amma yaki yin hakan, ya kuma fice daga madina yan kwanaki bayan haka. A cikin wasiyar da ya rubutawa kaninsa Mohammad alhanafiyya ya ce" Na yunkura ne don kawo gyara a cikin al-ummar kakana, Manzon Al..(s) Ina son yin umurni da kyawawa da kuma hana munanan ayyukan, da kuma bin sirar kakanaMohammad (s) da kuma babana Aliyu dan Abitalib (a) . Amma bayan watanni kimani 5 da yan kai da shi da sahabbansa duk sun yi shahada a kasar Karbala na kasar Iraqi.


02-Masu sauraron ko kun san cewa shekaru 134 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-Mayu-1882M. Robet Kokh wani masanin ilmin halittu masu rai dan kasar Jamus ya gano gwayar cutar tarin TB. Ko babban tari. Kokh yay i amfani da gilasai masu karfin gani ne wajen gano wannan kwayar cutar wacce ta kasha biliyoyin mutane a duniya.Cutar TB tana bayyana ne a lokacinda aka sami fari ko yunwa ko kuma wata cuta wacce ta gajiyar da jikin mutum. Wannan gagarumin aikin da Kokh yayi dai ya bude kofar gano maganin cutar da ma wasu cututtuka masu dangantaka da ita kamar cutar Maliria. Ya karbi kyautar Nobel a shekara ta 1905. An haifi Robert Kokh  a shekara ta 1843M, sannan ya rasu a ranar 27-Mayun-1910.