May 03, 2016 07:20 UTC

Yau Talata 14-Urdeebehesht-1395H.SH=25-Rajab-1437H.K=03-Mayu-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1254 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Rajab-183H.K. Limami na 7 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Al..(s) ya yi shahada. An haifi Imam Musa bin Jaafar (a) ne a garin Abwaa dake kuda da madina. Kuma ya kasance karkashin tarbiyan mahaifinsa har na tsawon shekaru 20. Bayan shahadar mahaifinsa ya jagorancin al-ummar kakakansa na tsawon shekaru 35. A cikin wannan lokacin ne Imam Musal Kazim (a) ya tarbiyantar da dalibai da dama wadanda suka watsu a cikin kasashen musulmi. Har'ila Imam Kazim(a) ya fuskanci matsaloli daga sarakunan Abbasiyawa da ya rayu da su. Daga cikinsu akwai Sarki Haruna Rasheed wanda ya jefa shi cikin kurkuku na tsawon shekaru 15, kuma a cikinsa ne aka bashi guma ya ci wanda ya kai ga shahadarsa. Muna taya al-ummar musulmi juyayin shahadar Imam Musal Kazim (a).

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 35 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Urdeebehesht-1360H.SH. Wani jirgin yakin gwamnatin Baath na kasar Iraqi ya kakkabo jirgin saman gwamnatin kasar Algeria wanda yake dauke ministan harkokin wajen kasar "Bin Yahyah" bayan wani ziyarar aiki da ya kawo nan birnin Tehran. A cikin bayanan da wani komiti na musamman wanda gwamnatin kasar Iran ta gudanar dangane da hatsarin, sun tabbatar da cewa wani jirgin yakin gwamnatin Sadam Husain ne ya kakkabo jirgin da ke dauke da Minista Bin Yahya ya kuma kasha shi.

Wannan hatsarin dai ya tabbatar da irin keta hurumin kasashen da gwamnatin kama karya ta Sadam Husain ta yi a kan kasashen yankin gabas ta tsakiya da dama. A lokacin hatsarin dai kasashen Iran da Iraqi suna cikin yaki wanda ya kai tsawon shekaru 8 ana tabkawa.

03-Daga Karshe Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 23 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Mayu-1993M. Hukumar bunkasa ilmi da al'adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO a takaice ta bayyana sanya ranar 23 ga watan mayu na ko wace shekara ta zama ranar duniya ta yan jaridu da nufin karfafa dokoki da kudurorin da suka bukaci incin bada bayanai da kuma watsa labarai a duk fadin duniya. A irin wannan rana ake tunatar da kasashen duniya da su kiyaye hakkin bada bayanai na kakafen yada labarai. Sai dai a bangare guda kuma kasashen yamma sukan yi amfanin da wannan damar don yada hutuna, da kuma watsa labarai wadanda suke kata hurumin wasu, musamman addinin Al…a bayan kasa. Sai dai kuma da wani zai soki HKI a wadan nan kasashe to bashi da damar yin hakan.