Ko Kun San Na (57) 26 Urdeebehesht Shekara Ta 1395 Hijira Kamaria
Yau Lahadi 26-Urdeebehesht-1395H.SH=08-Shaaban-1437H.K.=15-Mayu-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 97 da suka gabata wato 15-Mayun-1919M. Bayan wani yakin da aka yi a birnin Ezmir mai tarihi a kasar Turkia, tsakanin gwamnatin Musatafa Kamal Atatur wana ya rusa daular Usmania ya kuma kafa kasar Turkia da kuma gwamnatin kasar Girka wacce take iko da birnin, sojojin Turkia sun amamaye birnin.
Birnin Ezmir dai tana da tsohun tarihi a yankin, sannan tana bakin Teken Aje wanda yake da matukar muhimmanci a bangaren harkokin tsaro ga kasar ta Turkiya.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 76 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Mayun-1940M. A farkon yakin duniya na biyu sojojin Nazi na kasar Jamus sun mamaye kasar Holand bayan wasu hare hare masu tsanani da ta kai kan kasar na tsawon kwanaki biyar kacal. A ranar 10 ga watan mayu ne wancan shekarar ne sojojin na Jamus suka fara kai hare hare kan kasashen Faransa, Beljika, Holanda da Luxamburg daga kudancin kasar. A cikin kwanaki biyar da mamaye Holanda, sannan a cikin wasu Karin kwanaki ta mamaye sauran kasashen. Kafin mamayar kasar dai sarauniyar Wilihelmino ta kasar da gwamnatinta sun arce zuwa kasar Britania inda suka kafa gwamnatin 'yentaccen kasar Holanda a can har zuwa lokacinda aka sojojin kawance suka sake kwato kasar daga hannun jamusawan a shekara 1945M.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 23 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Mayun-1993M. Babban zauren majalisar dinkin duniya ta sanya ranar 15 ga watan mayu na ko wace shekara ta zama ranar iyali ta duniya. Manusafar sanya wanna ranar it ace kare Iyali daga duk wani abinda zai gurbata shi na daga mummunan tarbiyya da halaye, a matsayinta na asasin al-umma. Idan ta lalace haka nan al-umma zata lalace. Iyali sun hada da mata da muji da yara, wani lokacin har da kakanni, nan ne wurin samun nutsuwar ma'aurata sannan a nan ne ake renon yara. Don haka Kare ta daga wadan nan musibu shi ne zai samar da nagartacciyar al-umma a cikin duniya. Rabuwan iyaye musamman a kasashen yamma inda abin ya zama ruwanda dare yana lalata tarbiyyan yara, da haka kuma yake lalata al-umma ta gaba.