May 12, 2016 10:43 UTC

Yau Litinin 27-Urdeebehesht-1395H.SH=09-Shaaban-1437H.K.=16-Mayu-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 100 da suka gabata a rana irin ta yau wato turawan Ingila da faransa yan mulkin mallaka bayan yankin duniya na daya da kuma faduwar daular Usmania a hannunsu, sun zauna sun yi watandar kasashen yankin gabas ta tsakiya da kuma yankunan da suka kasance karkashin daular usmania kafin faduwarta a tsakaninsu. Yerjejeniyar ce ta rarraba kasashen Larabawa da wasu kasashen Asia ta yanzu. Wannan yerjejeniyar ta warware alkawulan da turawan suka yiwa kasashen Larabawa na cewa zasu basu iko da kasashen larabawa gaba daya idan sun taimaka masu wajen wargaza daular Usmania. Turawan sun yi amfani da bambance bambance tsakanin musulmi na mazhaba, kabilanci da sauransu don rabasu da daular Usmania.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 19 da suka gabata a rana irin ta yau wato 16-Mayu-1997M. shugaba mobuto sese seko na kasar Za'ir ya tsere daga kasarsa bayan da mayakan yan tawayen karkashin Laurant Kabila suka karato babban birnin kasar Kampala.
Mobuto yah an kan kujerar shugabancin kasar ne a shekara ta 1965 bayan ya jagoranci wani juyin mulki. Kasar Za'ir dai tana da arzikin ma'adinai wadanda suka hada da Luluu da zinari, don haka ne kasashen yamma suke dasawa da shi duk da cewa azzaluman shugaban ne. Bayan kwana guda da arcewarsa daga kasar sojojin Kabila sun kwace iko da birnin kinsasa sannan Launrant Kabila yah au kan kujerar shugabancin kasar. San nan ya canza sunan kasar daga Za'ir zuwa Congo Democradia.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 7 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Urdeebehesht -1388H.SH. Aya. Mohammad Taqi Bahjatee daya daga cikin manya manyan malaman addinin da kuma irfani ya rasu a nan Iran. An haifi Aya. Bahjati Fumi a garin Fuman na jigar Gilan a arewacin kasar, bayan kamala karatun sharer fage ya je Birnin Najaf na kasar Iraqi inda ya yi karatu a gaban manya manyan malamai na kasar.Aya. Bahjat ya dawo birnin Qum na kasar Iran inda yake bada darasin Bahsul khariz da kuma tarbiyyan Dalibai. Aya. Bahjati ya shahara da sanin ilmin Irfan da kuma tarbiyan dalibai. Banda haka Aya. Bahajati ya rubuta littafai wadanda suka hada da «کتاب الصلاة»، «جامع المسائل»، «وسیلة النجاة»