May 12, 2016 10:50 UTC

Yau Talata 28-Urdeebehesht-1395H.SH=10-Shaaban-1437H.K.=17-Mayu-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa yau ce 28-Urdeebehesht na wannan shekara, wato ranar girmama masani, marubucin wakoki sannan masanin ilmin irfani Hakim Umar Khayyam. An haifi abul fatahi Umar bin Ibrahim Khayyam Nishaburi afarkon karni na 6 hijira kamaria, wato tshanin shekara 417 zuwa 440 a garin Nishabur a arewa maso gaban kasar Iran. Umar Khayyam ya fi shahara da rubutattun wakokinsa kan ilmin irfani da falsafa. Don kayatarwansu ya sa an tarjamasu cikin harsuna da dama a duniya. Khayyam ya yi zurfi a cikin ilmin lissafi da taurari, har'ila yau ya rubuta littafai da dama a fanonin ilmi masu yawa. Daga cikinsu akwai «رساله فی کلیات الموجود»، «نوروز نامه » و «رساله فی طبیعیات».
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 151 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Mayun-1865M. Wakilan kasashen duniya kimani 20 sun rattaba hannu a karon farko kan yerjejeniyar sadarwa ta duniya da kuma dunkulewar kafar sadarwa da telegraph ta zama ta kada da kasa a birnin Paris na kasar Faransa. Da wanna dalilin ne aka zabi ranar, wato 17-mayu na ko wace shekara a matsayin ranar sadarwa da duniya. Sai kuma a shekara 1932, a wani taron da aka gudanar a birnin Madrid na kasar Espania aka sauya sunan dunkulelliyar kafar sadarwa ta kasa da kasa wato " International Telecommunication Union "ITU. Sannan a shekara ta 1947 wato bayan yankin duniya na biyu da kuma kafa majalisar dinkin duniya aka maida hukumar ITU karkashin kula na majalisar dinkin duniya. 
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 77 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Mayu-1939M. Gwamnatin kasar Britania ta lokacin, wacce kuma take mamaye da kasar Palasdinu, ta fidda wata sanarwan wacce ta kira "Farar takarda". Inda a ciki ta bayyana anniyarta na kafawa yahudawa a kasar Palasdinu. Ta bukaci a kafa kasashe biyu, daya ta yahudawa daya kuma ta musulmi a cikin shekaru goma masu zuwa. Takardan ta kara da cewa kafin shekara ta 1944 wasu Karin yahudawa dubu dari zasu yo hijira zuwa Palasdinu, sannan daga baya, hijirarsu sai da yardarm Palasdinawa. Wannan dai wata dubura ce ta kwace kasar Palasdinu da kuma kafa HKI a cikinta. Sai dai bangarorin biyu duk sun ki amincewa da wannan shawarar. Yahudawan sun bukaci HKI a cikin dukkan kasar Palasdinu da ma wasu yankunan kasashen larabawa.