Ko Kun San Na (60) 29 Urdeebehesht Shekara Ta 1395 Hijira Kamaria
Yau Laraba 30-Urdeebehesht-1395H.SH=11-Shaaban-1437H.K.=18-Mayu-2016M
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1404 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Shaaban-33H.K. Aka haifi Aliyu bin Husain, babban dan Imam Husain (a) a madina. Aliyu ban Husain ya kasance mai kama da kakansa manzon Al..(s) a halittarsa da kuma halayensa. Aliyu bin Husain yana da wasu kanne masu suna Aliyu don haka ne ake kiransa Aliyu Akbar, wato Aliyu babba. Wani abu mai muhimmanci a rayuwar Aliyu bin Husain shi ne yadda ya kasance tare da mahaifinsa Imam Husain (a) a yakin Karbala a shekara ta 61 H.K. ya yaki sojojin Yazid dan Mu'awiya har yayi shahada a gaban mahaifinsa. A nan kasar Iran ranar haihuwar Aliyul Akbar it ace ranar matasa.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 367 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Shaaban-1070H.K. Mohammad Taqi Majalisi , wanda ya fi shahara Majlisi na farko. An haifi Allamah Majlisi a shekara ta 1003 a birnin Esfahan , wanda ya kasance babban birnin daular safawiyawa a lokacin. Majlisi ya tashi a gaban iyayensa masu ilmi, don haka ya kamala karatun sharara fage a wajensu. Sanan ya je birnin Najaf na kasar Iraqi inda ya kammala karatunsa a gaban manya manyan malamai na lokacin wadanda suka hada a Sheikhul Bahaee. Allamah majlisi ya yi zurfi a cikin ilmin arfan ta yadda ya zama babban marjaee a cikin al-ummar shia. Ya kuma tarbiyantar da dalibai da dama wadanda suka hada da Mohammad Baqir Majlisi dansa na cikinsa. Wanda ya rubuta littafin Biharul anwar. Allamah Majalisi ya rubuta littafai da dama wadanda suka hada da «اربعین»، «شرح زیارت جامعه» و «روضة المتقین».
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 33 da suka gabata a rana irin ta yau wato 29-Urdeebehesh-1362H.SH. gwamnatin baath ta kasar Iraqi karkashin shugabancin sadam Husain ta kama mutane 90 daga cikin dangin Aya. Sayyeed Hakim a kasar, sannan bayan yan kwanaki ta kasha 6 daga cikinsu. Bayan wani lokaci ta sake kasha wasu mutane 10 daga cikin Dangin Aya. Sayyeed Hakim. Wani abin lura shi ne mafi yawan dangin Aya. Hakim malaman addini ne kuma mutanen kasar Iraqi suna mutuntasu matuka. Don haka ne gwamnatin Baath ta kasar ta ji tsorin samuwar wadan nan malaman addini a cikin mutanen kasar.