May 17, 2016 13:01 UTC

A shirin na yau zamu maida hankali ne kan ciwan Asma, daya daga cikin nau’o’in cututukan dake janyo matsalar rashin yin numfashi yadda ya kamata ga dan adam, wanda idan ma yayi tsanani a wasu lokutan yake kaiwa har ga rasa rai

Ciwon asma dai wani ciwo ne na huhu dake janyo matsalar rashin yin numfashi yadda ya kamata.

 Yakan janyo matsalar rasa rai ma a wasu lokutan idan abin yayi tsanani.  

Ciwan Asma yana shafar kowane jinsi na mutane, farare ne ko bakaken fata, kuma a kowane mataki na shekaru cikin kowace kabila. Amma an yi amanna cewa mutane matalauta ne suka fi yawa wajen fama da wannan matsala. 

Shi dai Ciwon kan zauna a jikin dan Adam yayi lamo na wani lokaci kafin a gane, kuma yakan iya faruwa kusan ga kowa daga kowane mataki na shekaru har zuwa karshen rayuwa. 

Amma a lokacin da ciwon ya motsa, kafofin shigar iska a jikin dan Adam kan rufe ta yadda za’a samu matsalar numfashi, Wato huhu zai samu karancin iskar da ta dace ya shaka. 

Matsalar asma tana cikin matsalolin da kan hana mai fama da ita rayuwarsa ta yau da kullum.


Tags