Ko Kun San Na (61) 30 Urdeebehesht Shekara Ta 1395 Hijira Kamaria
Yau Alhamis 30-Urdeebehesht-1395H.SH=12-Shaaban-1437H.K.=19-Mayu-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 91 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Mayu-1925M. Aka haifi Malcom X shugaban masu gwagwarmaya na bakaken fatar Amurka. Malcom X ko Malik Shabbas yana dan shekara 4 a duniya wata kungiyar yan ta’adda ta wariyar launin fata Kukulukus-kilon ta kona gidansu. Ya shiga makaranta, amma don matsalolin talaici ya bar karatu yana dan shekara 15 a duniya. Bayan haka yayi aiki a wani gidan cin abinci, inda a nan ya shiga shan kwayoyi da kuma sata. Daga karshe an daure shi shekaru 5 a gidan yara yana dan shekara 21 a duniya. A cikin gidan yari ne ya hadu da wasu musalmai bakaken fata wadanda suka nuna masa addinin musulunci da kuma shugaban musulman Amurka Alaija Mohammad. Bayan ya kamala kaso ya shaku da Alaija Mohammad da sauran musulmai wadanda suka koya masa addinin Musulunci. Malik shabbas ya na kwazo a cikin harkar addini wanda ya kai gay a gina masallatai a biranen Philadephia da kuma Detroit na kasar ta Amurka. Sai kuma a shekara ta 1964 ya ziyarci wasu kasashen Afrika da kuma Asia inda ya hadu da musulmai a can. Amma bayan dawowarsa Amurka da watannin ukku kacal aka kashe shi a birnin NewYork a ranar 21-Febrerun -1965M yana dan shekara 40 a duniya.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 81 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Mayun-1935M. Thomas Edward Lawrence, wanda aka fi saninsa a kasashen larabawa da suna “Lawrence Saudia” ya halaka sanadiyyar hatsarin mota. An haifi Lawrence a shekara ta 1888M, ya fara shigowa kasashen larabawa a shekara 1910M a cikin tawagar masu binciken tarihin kasashe. Sai kuma a shekara 1916 ya fara aikiwa ma’aikatar harkokin wajen Britania kan ayyukan liken asiri a kasashe Palasdinu Iraqi da Syria da kuma Saudia. Lawrence ya taimakawa turawan Ingila da Faransa wajen ingiza larabawa yin bore wa daular Usmania. Sannan bayan yakin duniya na daya, da kuma faduwan daular Usmania shi ya taimaka wajen dora sarki Abdulazeez a kasar saudia, sarki Sarki Abdullahi a kasar Jordan da kuma Faisal a kasar Syria. Lawrence ya rubuta wadan nan bayanai a littafinsa mai suna “Tawaye a cikin Hamada” .
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 30-Urdeebehesht-1361H.SH. Aya. Hashimi Rafsanjani, wanda ya kasance shugaban majalisa shoora –ialami a lokacin ya bada shawarar kafa Jami’ar –Ozod Islami, wanda daga bayan ya sami amincewar Imam Khomai (q) har ma ya bada gudumawar kudade don aiwatar da shirin Kafa Jami’ar. Bayan kamala dukka shirye shirye an kafa Jami’ar a ranar 27-Khurdod-1361H.SH. A halin yanzu dai Jami’ar Ozozd –Islami ce jami’a mai zaman kanta mafi girma a Iran. Sanna tana da rassa a ciki da wajen kasar.