May 19, 2016 22:20 UTC

Yau Jumma'a 31-Urdeebehesht-1395H.SH=13-Shaaban-1437H.K.=20-Mayu-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 114 da suka gabata a rana irin ta yau wato 20-mayun-1902M. Kasar Cuba ta shelanat sanub ‘yencin kai daga mamayar Amurka. Kafin haka dai tun shekara ta 1492M ne turawan espania suna mamaye kasar, wanna halin ya ci gaba har shekara 1894M a lokacinda Amurka ta tallafawa kungiyoyin kwatar ‘yencin kan kasar suka kore turawan Espania da kasar. Sai dai Amurka ta maye gurbin Turawan Espania a mamayar kasar ta Cuba, wannan yana kunshe hatta a cikin kundin tsarin mulkin kasar ta Cuba wanada aka rubuta a shekara ta 1902M.Wannan halin ya ci gaba har zuwa lokacinda Fudal Castro ya jagoranci wani tawaye wanda ya kawo karshe ikon Amurka a shekara a shekara 1959M. Amma Amurka ta maida kasar Cuba saniyar ware har na tsawon fiye da shekaru 50 kafin kasashen biyu su maida huldan jakadanci a cikin yan watanni da suka gabata.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 82 da suka gabata a rana irin ta yau wato 20-Mayu-1934M. Bayan da sarki Imam Yahaya na kasar Yemen ya sha kaye a yakin da ya shiga da kasar saudia, ya kulla wata yerjejeniya da sarki Abdul-aziz, inda a ciki Imam Yahaya ya amince ya mikawa kasar saudia yankunan Najran, Jeezan da kuma Aseer masu arzikin man fetur na tsawon shekaru 40. Amma bayan barkewan yaki da kuma rabuwar Yemen zuwa Yemen ta arewa da kuma Yemen ta Kudu kasar saudia ta taimakawa yeman ta arewa a yankin. Sai kuma duk da cewa alkawarin shekaru 40 da suka cimma da Imam Yahayah ta cika a shekara 1974M amma Yemen ta arewa bata data maganarba. Sai kuma bayan sake dunkulewar kasashen biyu a shekara ta 1990M maganar wadan nan yankunan sun sake tashe. Da wannan dalilin ne kasar saudia ta hada gangamin kasashen Larabawa don yakar gwamnatin kasar Yeman a shekara 2015M don dorawa Karen farautarta kan mutanen kasar Yemen wanda zai kasha maganar maido da wadan nan yakunan masu arzikin man fetur mallakin kasar ta Yemen.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 53 da suka gabata a rana irin ta yau wato 20-Mayun-1963M. Aka gudanar da taro na farko tsakanin shuwagabannin kasashen Afrika a birnin Adis Ababa na kasar Ethiopia (Habasha). Wanda sanadiyarsa aka kafa kungiyar hada kan kasashen Afrika OAU. Kafin haka dai babu wani abu da ya hada kasashen wadanda turawan yan mulkin mallaka suke mamaye da su. Manufar kafa kungiyar dai sun hada da taimakwa kasashen da suke karkashin mulkin mallakan turawa samun ‘yencin kai, raba gardama tsakanin kasashen kungiyar da kuma bunkasa harkokin tattalin arziki siyasa da kuma al-adu a tsakaninsu. Tare da taimakon kungiyar mafi yawan kasashen Afrika sun sami ‘yencin kansu a tsakanin shekaru 1960-1970M. Sai kuma a shekara ta 2000 M kungiyar hada kan kasashen Afrika ta rikide ta zama tarayyar Afrika, wacce aka samar da Majalisar tarayyar Afrika, komitin tsaro da kuma wasu rassa masu yawa.