Ko Kun San Na (63) 01 Khurddo Shekara Ta 1395 Hijira Kamaria
Yau Asabar 01- Khurddo -1395H.SH=14-Shaaban-1437H.K.=21-Mayu-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa yau ce 01-Khurdod na wannan shekara ta 1395H.Sh, ranar girama Sadruddeen Mohammad Shirazi wanda aka fi saninsa da Mulla Sadraa, ko kuma sadrul-Muta’allihin. An haifi Mulla Sadra a ranar 9-Jamada’ula-980H.K. Ya yi karatu a gaban manya manyan malamai na zamaninsa wadanda suka hada da Sheikh Bahaee da kuma Mirdamaad. Wani abu mai muhimmancina rayuwar Mulla Sadra shi yadda ya raya ilmin falsafa ta addini, ko Erfan bayan fahinci Falsafar إشراق da ta مشاء da kuma ta محيي الدين العربي , inda ya fara karantar da wani fannin ilman falsafa ta musulunci wacce ake kira حكمة المتعالية Mullah Sadra ya rubuta littafai sun kai 40, mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne أسفار الاربع . Mulla Sadra ya rasu a shekara ta 1050H.K. yana dan shekara 70 a duniya a birnin Basra na kasar Iraqi.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Khurdod-1359H.SH. Gwamnatin kasar Amurka ta soma dorawa Jumhuriyar Musulunci ta Iran takunkumin tattalin arziki. Bayan nasarar juyin juya halin musulunci a Iran gwamnatin Amurka ta rasa da dama daga cikin bukatunsa a kasar, don bayan ta kara shawo kan juyin ta koma kan matsin tattalin arziki don cimma bukatunta. Amma Imam Khomaini (q) wanda ya jagorancin juyin musulunci zuwa ga nasara ya bukaci mutanen kasar Iran kada su ji tsorin takunkumin tattalin arziki wanda Amurka ta dorawa kasar. Ya kuma kara da cewa “Sam Kada ku ji tsorin takunkumi, don idan sun sanya mana takunkumi, a nan ne zamu nemi tsayawa da kafafummu da kammu, don haka takumkin tattalin arzikin zai amfane mu ne”.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 25 da suka gabata a rana irin ta yau wato 21-Mayun-1991M. An kashe Rajeef Ghandi tsohon Priministan kasar India. An haifi Rajeef ne a shekara ta 1944M abirnin Bombay, ya tashi a gidan kakaknsa Jawahir Nero, priministan kasar India na farko bayan samun ‘yencin kai. Rajeef ya koyi tukin jirgin sama a jami’an Cambrage na kasar Britania. Sannan ya shiga harkokin siyasa ne a shekara 1983M sannan ya kisan mahaifiyarsa Indira Ghandi a shekara 1984 ya maye gurbinta a kan kujerar Priministan kasar. An kasha Rajeef Ggandi a ranar 21-Mayun-1991M a lokacinda ya je yakin neman zabe a kudancin kasar India yana dan shekara 47 a duniya. An kasha shi ne da bom wanda aka sa a cikin fulawan da aka dora masa a wuyarsa a lokacin yakin neman zaben.