Ko Kun San Na (64) 02 Khurddo Shekara Ta 1395 Hijira Kamaria
Yau Lahadi 02- Khurddo -1395H.SH=15-Shaaban-1437H.K.=22-Mayu-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1182 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Shaaban-255H.K. Aka haifi Imam Mahdi (a) dan Imam Hassan al-askari a garin Samira na arewacin birnin Bagdaza na kasar Iraqi. Sunansa shi ne sunan manzon Al…(s) sannan an fi saninsa da Imam Mahdi. Ya gudanar da shekaru biyar na farko a rayuwarsa a gaban mahaifinsa Imam Hassan al=askari (a). sanna bayan haka ya shiga gaiba karama ta shekaru 69 inda yake hulda da mabiyansa ta hannun jakadunsa guda hudu. Amma bayan rasuwar jakadansa na hudu ya shiga gaiba tare da umurnin All…ta’ala sannan shi kadai ya san sanda ya dace ya bayyana don cik duniya da adalci bayan cikarta da zalunci. A nan kasar Iran dai ranar haihuwarsa itace ranar raunana ta duniya. Dukkanin musulmi sun yi imani da Imam Mahdi (a) sai dai sun saba ne kawai wajen lokacin haihuwarsa.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1108 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-shaaban-329H.K. Aliyu binMohammad Samari jakadan Imam Mahdi (a) na hudu ya rasu. Kafin gaiban Imam Mahdi (a) daga ganin mutane dai ya nada jakadu 4, wadanda yake mu’amala da mabiyansa ta hannnunsu. Aliyu bin Mohammad Samari shine jakadansa na karshe wanda ya bashi sakon cewa bayan mutuwarsa ba zai nada wani jakada ba, sannan mabiyansa su koma ga mahaddata hadisan iyalan gidan manzon Al..(s) wato malamai don neman shiriya, ya sanyasu hujjoji a kan mutane sannan shi hujjar All..ne. Mabiyansa dai zasu ci gaba da gwagwarmaya don samar da yanayin da zai bada dama ga bayyanarsa don kauda zalunci a bayan kasa.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 26 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Mayun-1990M. Ministocin harkokin waje na kasashen Yemen ta Arewa da Yemen da Kudu sun bada sanarwan hadin guiwa na sake dunkulewar kasashen biyu zuwa Jumhuriyar Yemen. Wannan ya share fagen samar da majalisar hadin kan kasashen biyu wacce ta rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar. Wani abin lura dangane da kasar Yemen shi ne cewa, a shekara 1914M. ne a wata yerjejeniya tsakanin daular Usmania da kuma turawan Ingila, daular usmania ta amincewa turawan raba kasar Yemen biyu.