Ko Kun San Na (65) 03 Khurddo Shekara Ta 1395 Hijira Kamaria
Yau Litinin 03- Khurddo -1395H.SH=16-Shaaban-1437H.K.=23-Mayu-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 101 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Mayun-1915M. Kasar Italia ta shiga yakin duniya na daya. Shigar kasar Italia yakin dai ya kawo sauye sauye masu yawa a nahiyar Turai. Da farko dai ta fadawa kasar Austria da yaki, sannan ta kara fadadashi zuwa daular Usmania. Sai dai duk da cewa kasar Italia tana bangaren kawancen da suka sami nasara a karshen yakin, amma don asarorin sojoji kimani miliyon 5.5 da tayi ya maida ita cikin kasashen da suka yi asara a yakin. Don bayan yakin kasashen Ingila da faransa ne suka yi watandar yankuna daular Usmania da suka wargaza a yakin.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 67 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Mayu-1949M. Kasashen Faransa, Amurka da kuma Britania wadanda suke mamaye da wasu yankuna kasar Jamus bayan yakin duniya na biyu sun bada sanarwan kafa kasar tarayyar Jamus ta Yamma mai headquter a birnin Bon. Bayan yakin duniya na biyu dai tarayyar Soviet ta mamaye Jamus ta gabas a yakin wadannan kasashe ukku suka mamaye wasu yankuna kasar daga yamma. Wanna ya jawo sabani kan irin siyasar da za’a aiwatar a kasar, shi ne daga karshe kasashen ukku suka shelanta tarattar Jamus ta Yamma. Sanna suka kafa kungiyar tsaro ta NATO suka kuma jibge sojojinsu a cikin tarayyar Jamus ta yamma don fuskantar barazanar tarayyar Soviet. Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekara 1989 a lokacin da kasashen biyu suka sake dunkulewa.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Khurdod-1361H.SH. Sojoji da kuma mayaka masu sa kai na Jumhuriyar musulunci ta Iran sun sami nasara dawo da ikon gwamnatin kasar a birnin Khuramsha dake kudu maso yammacin kasar bayan mayar da sojojin Sadam Husain na kasar Iraqi suka yiwa birnin na tsawon watanni 20. A shekara ta 1359 H.SH ne sojojin Sadam suka mamaye birnin Khuramsha babban birnin lardin Khuzistan, kuma tashar jiragen ruwa babba wacce a nan ne kogunan Kaarun da Arwanda suka hadu.
Dawo da wannan birnin hannu gwamnatin JMI dai ya zama mabudin dawo da dukkan yankun da sojojin sadam Husain suka mamaye a shekara ta 1359H.SH.