May 22, 2016 14:35 UTC

Yau Talata 04-Khurdod-1395H.SH=17-Shaaban-1437H.K.=24-Mayu-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 25 da suka gabata a rana irin ta yau wato 24-Mayu-1991M. Haramtacciyar kasar Israela ta fara aiwatar da wani shiri wanda ta kaira "Shirin Sulaimana" na jigilar yahudawan kasar Ethiopia 14,400 zuwa kasar Paladinu da suke mamaye da shi da sunan kyautata rayuwarsu. Banda haka a shekara ta 1984 ma yahudawan sun aiwatar da makamancin wannan shi ne mai suna "Shirin Musa" inda a wancan karon ma suka yi jigilar yahudawan Ethiopia wadanda aka fi sani da "Yahudawan Falasha" zuwa kasar Palasdinu da suka mamaye. Sai dai yahudawan na falasha basu sami abin kamar yadda suke tsamnani ba, don suna faskantar wariya daga sauran yahudawa fararen fata.


02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 23 da suka gabata a rana irin ta yau wato 24-Mayu-1993M. Kasar Eriteria dake arewa maso gabacin kasar Ethiopia ta sami 'yencin kanta daga Kasar ta Ethiopia. A shekara ta 1953 turawan Italia yan mulkin mallaka suka maida kasar Ereiteria karkashin kasar Ethiopia bayan mamayarta tun shekara 1936M. Bayan sake hada ta da kasar Ethiopia ne mutanen yankin Eriteria suka ki amincewa da hakan. Suka kuma sabi makami har zuwa lokacin da aka gudanar da zaben raba gardama a yankin suka kuma zabi 'yencin kai wanda ya tabbata a rana irin ta yau a shekara ta 1993M.


03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 16 da suka gabata a rana irin ta yau wato 24-Mayun-2000M. Sojojin yahudawan HKI sun fice daga kasar Lebanon sanadiyyar gwagwarmayan da kungiyar Hizbullah ta kasar ta yi ta yi da su. Yahudawan sun mamaye kar hari kan kasar Lebanon a karo na hudu a shekara 1978M, kuma a lokacin ne suka ware wani danki daga kudancin kasar wanda suka kira yankin tsaron israela suke kuma jibge sojojinsu a yankin. Amma bayan mamaya na tsawon shekaru 22 a dole suka fice daga kasar a rana irin ta yau wato 24-Mayu-2000. An kafa kungiyar Hizbullah ce bayan nasarar juyin juya halin musulunci a Iran a shekara 1979M. Kuma tun lokacin kafa ta take samun nasarori a kan yahudawan a ciki da wajen kasar ta Lebanon.