May 22, 2016 14:39 UTC

Yau Laraba 05-Khurdod-1395H.SH=18-Shaaban-1437H.K.=25-Mayu-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1111 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Shaaban-326H.K. Abul-Kasim Hasain bin Ruhu –Nubakhti jakadan Imam Mahadi (a) na ukku ya rasu. Nubakhti babban malamin hadisi ne ya kuma kware wajen jayeyye da da masu husuma da mabiya Ah-lulbait (a). Nubakhti ya yi aikin jakadanci tsakanin Imam (a) da mabiyansa ne tsakanin shekaru 305-326H.K. Kafin rasuwar jakada na biyu Mohammad Usman da shekaru biyu zuwa ukku yakan karbi kudaden da suke wajen wakilansa don ajiyarsu a wajen Nubakhti , wanda da haka ya share masa fagen zama jakadan Imam (a).


02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 113 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Shaaban-1324H.K. Aka bude majalisar dokoki ta farko bayan juyin juya halin da aka fi sani da Mashrudia a nan Iran. A karon farko wakilan wannan majalisar mutane suka zabe su kai tsaye. Sannan fittun malaman addini wadanda suka hada da Sayyeed Muhammad Tabatabai da kuma Sayyeed Abdullahi Bebahani. Bayan bude majalisar ne aka rubuta kundin tsarin mulkin kasar Iran na farko, sannan daga baya ya sami sanya hannun sarki Muzaffadeen Kajar na lokacin.


03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 53 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Mayu-1963M. Shuwagabannin kasashen Afrika 30 sun rattaba hannu kan yerjejeniyar kafa kungiyar hada kan kasashen Afrika OAU a birnin adis Ababa na kasar Ethiopia. Manufar kafa kungiyar OAU dai ita ce taimakwa sauran kasashen nahiyar wadanda suke karkashin mulkin mallakar turawa samun'yencin kai, da kuma warware sabanin da ke tasowa tsakanin kasashen. Sai kuma a shekara ta 2002M a wani taron da shuwagabnnin kasashen kungiyar suka gudanar a birnin Durban na kasar Afrika ta kudu sun canza sunan kungiyar zuwa "Tarayyar Afrika".