Ko Kun San Na (68) 06 Khudod Shekara Ta 1395 Hijira Kamaria
Yau Alhamis 06-Khurdod-1395H.SH=19-Shaaban-1437H.K.=26-Mayu-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1431 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Shaaban-06H.K. Aka yi yakin Bani Mustalaq tsakanin rundunar musulmi da musrikan bani mustalq daga cikin kabilar Khuza'a. Bani mustalaq suna zane ne kusa da Makka sannan shuwagabanninsu masu bautar gumaka na cikin Kaaba ne. Bayan bayyanar musulunci da kuma kafa daular musulunci ta farko a madina, Bani mustalaq sun daura damarar yaki don karya mausulmi, amma All.. ya bawa musulmi sa'a sun sami nasara a kansu a rana irin ta yau.
02- Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 44 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-Mayu-1972M. shuwagabannin tarayyar Soviet ta lokacin da kuma na Amurka sun rattaba hannu kan yerjejeniyar takaita makaman kare danginsu a karo na farko wacce ake kira " Strategic Arms Limitation Talks ko kuma SALT1. Shugaba Richard Nixon na kasar Amurka da kuma tokoransa na tarayyar Soviet Leonid Brezhnev ne suka rattaba hannu kan yerjejeniyar wacce ta bukaci kasashen biyu su rage makaman linzaminsu masu cin gajere da matsakaici da dogon zango masu daukar kawukan nuklia. Da farko sun sanya sun debawa kansu shekaru 5 don aiwatar da yerjejeniyar daga baya suka kara wasu shekaru biyar. Sai dai duk da haka bayan da tarayyar Soviet ta mamaye lasar Afganistan a shekara 1979M shugaban kasar Amurka na lokacin Jeamy Carter ya jingine yerjejeniyar. Daga nan kuma kasashen biyu suka ci gaba da gasar kera makamai kamar da.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 35 da suaka gabata a rana irin ta yau wato 6-Mayun-1981M. Aka kafa kungiyar raya kasashen larabawa na yankin tekun Farisa. Kasashen wannan kungiyar dai sun hada da Saudia, Bahrai, Kuwait, Omman, Qatar da kuma Hadaddiyar daular Larabawa. Manufar kafa kungiyar shi ne aiki tare don tabbatar da tsaro a yankin da kuma bunkasa tattalin arziki da siyasar kasashen. Sai dai ganin cewa dukkan kasashen 6 sun dogara da kasashen waje don samar da tsaro a kasashensu, lamuran tsaro a yankin sai kara tabarbarewa yake a ko wace rana. Banda haka kungiyar ta ware wasu kasashen a yankin daga shiga kungiyar wanda ya kara raunanata.