Ko Kun San Na (69) 07 Khudod Shekara Ta 1395 Hijira Kamaria
Yau Jumma'a 07-Khurdod-1395H.SH=20-Shaaban-1437H.K.=27-Mayu-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1052 da suka gabata a rana irin ta yau wato 20-Shaaban-385H.K. Ibn Nadeem sanannen malamin tarihi a karni na 11 ya rasu. Ibn Nadeem ya shahara kan wani littafinsa mai suna «الفهرست» inda ya tattari fannonin ilmi masu yawa a cikinsa. «الفهرست» ya kunci tarihin ci gaban da aka sami a musulunci har zuwa zamanin rubuta shi. Banda haka Ibn Nadeem ya kawo tarihin malaman musulunci da kuma masu ilmi a wasu fannoni ban a addinin ba. Banda haka ya kawo manya manyan littafan da aka rubuta da kuma wadanda suka rubutasu har zuwa zamaninsa. Banda wannan littafin Ibn Nadeem yana da wani littafi mai suna «الاوصاف و التشبیهات».
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 56 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Mayun-1960M. Janar Jamal Goorsal ya jagoranci wani juyin mulki a kasar Turkiya wanda ya kai ga nasara ya kuma zaman shugaban kasar ta Turkia. Sanadiyar juyin mulkin dais hi ne boren da mutanen kasar suka yiwa gwamnatin Priminista Adnan Mundaris, wacce ta kara warware matsalolin tattalin arzikin kasar. Banda haka yayi amfanin da karfi wajen murkushe masu adawa da gwamnatin tasa. A cikin wannan halin ne Janar Goorsal ya rubuta masa wasika kan ya gabatar da sauye sauye a harkokin mulkin kasar amma ya yi watsi da gargadin. Sai kuma a ranar 29-Mayu na wancan shekarar aka yi masa juyin mulki sannan aka rataya shi bayan watanni ukku tare da laifin yin ammafani da ikonsa da inda bai dace ba.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 07-Khurdod-1359H.SH. Aka bude majalisar dokoki na Iran ta farko bayan samun nasara juyin juya halin musulunci. Kafa majalisar dai na daga cikin muhimman matakan samun tabbacin nasarar juyin da kuma tafiyar da kasar Iran karkashin tutar musulunci. Majalisar wacce ake kira shoora Islami tana da wakilai 290, wadanda mutane sukan zabesu kai tsaye sannan ko wani gari yana da wakilai gwagwadon yawan mutanenta. Banda haka hatta kananan addinai da mazhabobi wadanda yawansu ya kai dubu 150 kuma aka amince da samuwarsu suna da wakilai a majalisar. Aikin majalisar shoora Islami dai sun hada da samar da dokoki da kuma sanya ido a kan ayyukan gwamnati.