Ko Kun San Na (70) 08 Khudod Shekara Ta 1395 Hijira Kamaria
Yau Asabar 08-Khurdod-1395H.SH=21-Shaaban-1437H.K.=28-Mayu-2016M
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 76 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Mayu-1940M. A farkon yakin duniya na biyu sojojin Naza na kasar Jamus sun farwa kasar Beljium da yaki duk da cewa ta bayyana rashin shiga wani bangare a yakin. Bayan fara yakin da kwanaki ukku sojojin Jamus sun mamaye birnin Brussels. Banda aka a dai dai lokacinne sojojin Nazan suka kai farmaki kan kasar Faransa inda suka kasha sojojin kawance kimani dubu 50 a cikin kwanaki ukku suka kuma lalata jiragen yakinsu kimani 400 wannan ya tilastawa sojojin kawance janyewa daga kasar, inda sojojin Nazi suka karbi iko da dukkan kasar Faransa.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 52 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Mayu-1964M. Bayan amincewar kungiyar kasashen Larabawa an kafa kungiyar kwatar 'yencin Palasdinawa ta PLO. An kafa kungiyar ne tare da dunkulewar wasu kananan kungiyoyin kwatar 'yencin Palasdinawa kimani 8. Sai kuma bayan shekara guda aka samar da reshen mayaka ta kungiyar wanda ake kira Fatah mai dakaru kimani 10,000. Sai kuma a shekara 1974M PlO ta zama memba mai sanya ido a majalisar dinkin duniya. Zuwa shekara ta 1982 PLO tana da ofisoshi a kasashe kimani 100 a duniya. Amma kuma a shekara ta 1982 ne, sojojin HKI suka mamaye kasar Lebanon suka kuma tilastawa kungiyar PLO ficewa daga kasar. Daga nan ne a hankali a hankali kungiyar ta fara dawowa daga rikiyar daukar makami don yakar yahudawan Israela. A shekara 1993 shugaban kungiyar Yasar Arafat ya rattaba hannu kan takardun sulhun Oslo tare da HKI, tare da alkawarin zata bada cin gashin kai ga Palasdinawa daga Gaza zuwa Irisha, alkawarinda yahudawan basu ciki ba har yau.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 18 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Mayu-1998M. Kasar Pakistan ta gwada makaman nukliarta a karon farako har sau biyar. Wannan gwajin ya zo ne makonni biyu kacal bayan da kasar India abokiyar hamayyarta ta gwada nata makaman na Nuklia. Gwajin kasar Pakistan dai ya fusata turawa da kuma Amurka wadanda suka dorawa kasar Pakistan takunkumai. Banda haka duk kokarin da kasashen suka yin a kasar Pakistan da shiga hukumar IAEA ta kula da makaman nuklia a duniya ta ki yin hakan.