Jun 07, 2016 00:46 UTC

Yau Alhamis 20-Khurdod-1395H.SH-03-Ramadan-1437H.K.=09-Yuni-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1024 da suka gabata a rana irin ta yau wato 03-Ramadan-413H.K. Mohammad bin Numan wanda aka fi saninsa da Sheikh Al-Mufid daya daga cikin manya manyan malaman addinin na mazhabar iyalan gidan manzon Al..(s) ya rasu. Sheikh Al-Mufid yak ore a cikin ilmomi da dama, sannan shi ne ya shimfida harsashen wasu ilmomin, wadanda suka hada da ilmin kalam, inda a karon farko shi ne ya taba wallafa littafi a kansa. Banda haka Sheikh Al-Mufid yakan yi muhawara da malaman sauran mazhabobin musulunci ya kuma bayyana masu wasu abubuwan da suke boye a cikin mazhabarsu wadanda basu sani ba. Sheikh Al-Mufid ya wallafa littafai wadanda yawansu ya kai 200 fitattu daga cikinsu sun hada da  «الکلام فی دلائل القرآن»، «الارکان» و «کشف السرائر».

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 131 da suka gabata a rana irin ta yau wato 09-Yuni-1885M. Sojojin kasar Jamus sun mamaye kasar Togo a yammacin Africa. Turawan Jamus sun yi amfani da kasar Togo a matsayin tashar jiragen ruwanta masu ciniki bayan daga kasar zuwa kasashen turai da Amurka. Don haka ne ma ake kiran kasar Togo da suna "Tashar bayi" a yammacin Afrika. Wannan halin ya ci gaba  har zuwa bayan yakin duniya na daya a lokacinda turawan Faransa suka maye gurbin turawan Jamus a wajen mamayar kasar ta Togo. Kasar Togo ta sami 'yencin kanta a shekata 1960M kuma tana da kasa mai fadin kilomita murabbaee dubu 56 . Har'ila yau tana makobtaka da kasashen Borkina Faso , Ghana da kuma Benin.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 35 da suka gabata a rana irin ta yau wato 20-Khurdod-1360H.SH. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa JMI ya kwace ikon babban komandan sojojin kasar Iran daga hannun shugaban kasa na farko bayan samun nasara juyin juya halin musulunci a kasar wato Bani Sadar. Tun bayan zabensa a kan kujerar shugabancin kasar Iran ne mani sadar ya fara nuna wasu halaye na munafurci, inda daga cikin yana hulda da makiya juyin juya hali sannan ya nisantar da matasa masu bin tafarkin Imam daga harkokin mulki. Banda hada Bani sadar ya ki amincewa da Dr Ali Rajai a matsayin Priministansa bayan da majalisar dokokin kasar ta zabe shi da babban rinjaye. Har'ila yau ha'incinsa ya bayyana a lokacinda sojojin sadan suka fara mamayar kasar Iran inda yaki tallafawa sojojin kasar da bukatunsa don hana sojojin sadam mamayar kasar. Bayan haka ne Imam ya shawarci mutanensa ya kuma rubuta umurnin kwace iko da rundunonin tsaron kasar daga hannun Bani Sadar. Bayan haka ne majalisar dokokin kasar  ta tsige shi daga kan kujerar shugabancin kasar a ranar 31=Khurdod-1360H.SH.