Ko Kun san na (83) 21 Khurdod Shekara ta 1397 Hijira Shamsia
Yau Jumma'a 21-Khurdod-1395H.SH-04-Ramadan-1437H.K.=10-Yuni-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 226 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Yuni-1790M. Sojojin turawan Ingila yan mulkin mallaka sun fara mamayar kasar Malasia. Kafin haka dai turawan Holanda ne suke mamaye da kasar. Amma bayan shigowar turawan Ingila a shekara 1824 M turawan Holand sun sulhunta da turawan Ingila kan zata barmasu kasar Malasia gaba daya sannan ita kuma Ingila ta bar mata kasar indonasia. Haka aka yi, inda yan mulkin mallakan suka ci gaba da kwasar dokiyoyin wadan nana kasashe biyu har zuwa shekasra 1957M a lokacinda kasar Malasia ta sami 'yencin kanta sannan Indonasia kuma shekara guda bayan haka.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 16 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Yuni-2000M. Shugaban kasar Syria Hafiz Al-Asad bayan rashin lafiya na wani lokaci ya rasu. An haifi Asad a shekara 1930. Bayan kamala karatu ya zama babban komandan sojojin Syria a shekara 1964, sai kuma shekaru biyu bayan haka yazama ministan tsaron kasar. Sannan a shekara 1970 ya jagoranci wani juyin mulki wanda ya kaishi ga zama shugaban kasa. Daga nan ya gudanar da zaben jin ra'ayin mutane so da dama wanda ya maida shi shugaban kasar siria na din din din. A yakin Larabawa da HKI a shekara 1967 Hafiz al-asad ne ministan tsaro, kuma a lokacinne HKI ta kwace tuddan Golan daga kasar Syria, amma ya sami nasarar dawo da wani bangare na yamkin a yakin shekara 1973. Wani abin lura a cikin siyasar Shugaba Hafizul Asad shi ne yaki amincewa ya tattauna da HKI kan matsalolin gabas ta tsakiya wadanda suka hada da Palasdinu da kuma mamayar da HKI tayiwa wasu kasashen larabawan.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa yau ce 10 –Yuni ranar da aka ware don sana'o'in hannu a aduniya. Bayan an kafa Majalisar dinkin duniya, majalisar ta mikawa hukumar UNESCO mai kula da ilmi da tarbiya da kuma kiyaye al-adu nauyin kare ayyukan ayyukan hannu da al-adun al-ummu aban daban na kasashen duniya. Da wannan dalilin ne hukumar Unesco ta kafa komitin kula da sana'o'in hannu don kare irin wannan sana'o'I bacewa a duniya. Wannan komitin tana kwadaitar da al-umma kiyaye al-adunsu da kuma sana'oin hannu don kada su bace, A halin yanzu dai komitin kare al-adu da kuma sana'oin hannu tana da cibiya a birnin Amstadam sannan kasashen duniya 90 ne suke membobin a cikin harkokin sana'o'in hannu.