Ko Kun san na (84) 22 Khurdod Shekara ta 1397 Hijira Shamsia
Yau Asabar 22-Khurdod-1395H.SH-05-Ramadan-1437H.K.=11-Yuni-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 161 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Yuni-1855M. Wasu masanan ilmin kimiyyar lissafi biyu yan kasar Jamus sun sami nasara rarraba hasken rana zuwa launukansa daban daban masu yawa. Masanan wato Kirchhoff ) (Bunse sun gudanar da bincike mafi yawa kafin su kai ga wannan natijar. Wani abin lura shi wadan nan masana guda biyu sun sami nasara gano launukan hasken rana da ke bayyana a sararin samaniya a lokacinda ake ruwan wato bakin gizo, inda suka gano adadin launukan da suke kunshe a cikin hasken na rana tare da amfani da wasu gilasai na musamman don yin wannan aikin. Da wannan ne kuma aka kawo karshe wasu tastuniyoyin kan bakan giza wanda al-ummu daban daban suke fadi a dunia.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 56 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Khurdod-1339H.SH. Babban malamin addini mai suna Mirza Mohammad Husain Fadle Tuni daya daga cikin manya manyan malamai a nan birnin Tehran ya rasu. An haifi Mirza Tuni a shekara ta 1257 H. SH garin Firdau a arewa maso gabacin kasar Iran. Mirza Tuni ya fara karatu a gida sannan ya fara yawatawa cikin fitattun malaman kasar Iran yana daukar karatu har ya zama baban malami. Bayan kamala karatu ya dawo nan Tehran da zama inda ya ci gaba da karantarwa da kuma wallafe wallafen littafai daga cikin litafan da ya rubuta akwai «حکمت قدیم»، «الهیات» و «حواشی بر اسفار»
03-Daga karshe masu sauraro ko kunsan cewa shekaru 23 da suka gabata a rana irin ta yau wato 22-Lkhurdod-1372H.SH. Wani jami'an diblomasia dan kasar Iran mai suna Rasul Muntaziri wanda yake aiki da ofishin jakadancin Iran dake birnin Zograb na kasar Koroshiya ya yi shahada a hannun wasu masu tsatsauran ra'ayi yan kabilar sabiwa a kasar ta Koroshia. Rasul Mantari dai yana daga cikin jami'an gwamnatin kasar Iran da suke tallafawa musulman kasar Busnia Hazogovina a yankin Balkan da yke faruwa a lokacin tsakanin kasashen Yuguslavia da makobtanta.