Ko Kun san Na (85) 23 Khurdod shekara ta 1395 Hijira Shamsia
Yau Lahadi 23-Khurdod-1395HpSH-06-Ramadan-1437H.K.=12-Yuni-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Khurdod-1359H.SH. Imam Khomaini (q) wanda wanda ya assasa Jumhuriyar musulunci ta Iran ya bada umurnin kafa wanta majalisar malamai kuma kwararru a fannonin ilmin daban daban don su samar da sauyi a tsarin karatu a cikin makarantun kasar Iran musamman Jami'oee da kuma manya manyan makarantun kasar. A cikin umurnin Imam ya bukaci majalisar ta tsarkake makaranatun kasar Iran daga al-adun turawa da wadanda basu dace da addinin musulunci ba. Su kuma gabatar da sauyi a tsarin makarantun na zahiri ta yadda zasu dace da karantarwan addinin musulunci. Majalisar mai suna "Majalisar shoora ta sauyin al-adu" ta sami masarori masu yawa kuma haryanzun tana ci gaba da aiki a wajen kara kyautata tsarin makarantun kasar Iran.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 33 da suka gabata a rana irin ta yau wato 23-Khurdod-1362H.SH. Malama Nusrat Amin babbar malamar addinin wacce ta kai matsayin mujtahidi ta rasu tana diyar shekara 97 a duniya. An haifi malama Nusrat Amin a birnin Esfahan na kasar Iran a shekara ta 1265H.SH. Kuma ta fara karatu a gaban iyayenta sannan ta shiga neman ilmi a gaban manya manyan malamai na zamaninat a birnin Esfahan har zuwa matsayin Mujtahidi. Malama Nusrat Amin ilmin sanin tafsirin Alqur'ani kuma ta wallafi littafai da dama a fannin, wanda ya hada da tafsirin al-qur'ani mai mujalladai 15. Har'ila yau malama Nusrat wallafa wasu littafai a fanin ilmin efani wadanda suka hada da «سیر و سلوک»، «راه خوش بختی» و «نفحات الرحمانیه».
03- Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 25 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Yuni-1991M. An gudanar da zaman shugaban kasa a karo na farko a tarayyar Rasha, don muhimmancin wannan ranar aka sanyata a matsayin ranar kasa a kasar ta Rasha. A cikin zaben dai Boris Yelson ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar tare da samun kasha 57% na yawan kuri'un da aka kada. A cikin watan Afrilun shekara 1990 ne majalisar jumhuriyar Rasha kafin wargajewar Tarayyar Soviet ta bada sanarwan cewa dokokin cikin Rasha ne suke da rinjaye kan dokokin tarayyar Soviet wanda hakan ya share fagen wargajeawar tarayyar ta Soviet a shekarar da ta biyo. Kasar Rasha dai tana da fadin kasa mai fadin kilomita murabba'ee miliyon 17 sannan tana da kasha 11% na fadin kasa a duniya, wannan ya maida ita kasa mafi girama a duniya, inda bangarorinta sun hada wasu bangarori na nahiyar Turai da Asia.