Ko Kun san Na (86) 24 Khurdod shekara ta 1395 Hijira Shamsia
Yau Litinin 24-Khurdod-1395H.SH-07-Ramadan-1437H.K.=13-Yuni-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1440 da suka gabata a rana irin ta yau wato 7-Ramadan-Shekara ta 10 bayan fara manzanci. Bisa wasu ruwayoyi Abutalib dan Abdulmuttalib ammin manzon All…(s) kuma babban mai kareshi daga cutarwan kuraishawa ya rasu a Makka. Bayan rasuwar kakan manzon All..(s) Abdulmuttalib renon manzon All..(s) dan shekara 8 a duniya a lokacin ya koma ga Abutalib, wanda ya kasance tare da shi a cikin dukkan marhaloli isar da sakon All.. har zuwa rasuwarsa a rana irin ta yau. Bayan rasuwar Abutalib ne Quraishawa suka zafafa cutar da manzaon Al…(s) wanda ya kai ga hijirarsa daga Makka zuwa madina a cikin shekaru biyu da suka biyo bayan rasuwar Abutalib.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1236 da suka gabata a rana irin ta yau wato 7-Ramadan-201H.K. Sarki Maamun dan Sarki Haruna Rasheed daya daga cikin sarakunan Abbasiyawa ya tilastawa Imam Aliyu bin Musa, wanda akewa Lakabi da (arrida) (a), wanda kuma shi ne limami na 8 daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon Al…(s), ya tialsta masa karban mukamin Sarki mai jiran gado. Kafin haka dau Sarki Maamun ya tilasta masa hijira daga Madina zuwa garin Maru na yankin Khurasan a nan Kasar Iran inda shi Maamun yake don ya sanya ido a kan ayyukansa. Sannan Maamun ya aura masa diyarsa Ummul Fadle, bana haka Maamun ya sauya alamar Abbasiyawa wato bakeken riguna zuwa ga na Alawiyawa wato Kore, don dai ya tabbatar da sajewar gidajen biyu. Amma Imam Rida (a) ya amince da matsayin da aka tilasta masa, amma kuma ya shaidawa Sarki Maamun hakan ba zai tabbataba. Bayan haka ne sai Maamun ya ga cewa matsayin da ya bawa Imam Rida (a) ya kara daukaka shi, harma yana jin tsoron in ya ga dama yana iya kwace ikonsa. Anan ne ya shayar da shi guba ya kuma kai shi ga shahada a ranar 30-Safar-203H.K.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 72 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Yuni-1944M. Sojojin kasar Jamus a yakin duniya na biyu sun cilla makamin linzami na farko da suka kera zuwa kasar Ingila. Makamin mai suna V-1. Kafin haka dai sojojin Naza suna amfani da jiragen sama ne kadai wajen kai hare hare zuwa Ingila don nisan da take da shi daga jamus don kuma ruwan tekun da ke tsakanin kasashen. Wannan shi ne makamin mai linzami na farko a duniya, sannan bayan yakin duniya na biyu manya manyan kasashen duniya sun kera wasu makamai masu linzami masu inganci sosai, wadanda ma suke iya daukar makaman kare dangi su kuke keta nahiyoyi da su.