Ko Kun san na (87) 25 Khurdod Shekara Ta 1395 Hijira Shamsia
Yau Laraba 25-Khurdod-1395H.SH= 08-Ramadan-1437H.K.=14-Yuni-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 196 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Yuni-1820M. Sojojin Kasar Masar tare da jagorancin Mohammad Ali Pasha sun farwa kasar Arewacin kasar Sudan da yaki, a dai dai lokacin ne kuma Sojojin Turawan Britania yan mulkin mallaka suka farwa kudancin kasar ta Sudan suka mamaye shi. Amma mutanen sudan karkashin jagorancin Mahdi Sudan sun yi turjiyan sojojin kasashen biyu daga shekara 1881 zuwa 1895. Sai dai bayan haka sojojin mamaya na kasashen Masar da Britania sun sami galaba a kansu a shekara 1898. Sanna bayan haka da shekara guda sojojin mamayan suka raba ikon sudan a tsakaninsu. Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekara 1956M a lokacinda kasar Sudan ta sami 'yencin kanta.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 98 da suka gabata a rana irin ta yau wato 25-Khurdod-1297H.SH. Aya. Sayyeed Mustafa Mujatahidy Kashani daya daga cikin manya manyan malaman addini a nan kasar Iran ya rasu. An haifi Aya. Mustafa kashani a garin Kashan da ke tsakiyar kasar Iran. Ya fara karatun sharara fage a gaban iyayensa malamai. Daga nan ya je birnin Najaf na kasar Iraqi inda ya kammala karatunsa a gaban manya manyan malamai na lokacin. Bayan ya sami shaidar Injtihadi ya fara karantarwa da wallafe wallafe. Wani abu mai muhimmanci a rayauwar Aya. Kahani yana daga cikin malamai wadanda suka yi gwagwarmayan da zaluncin sarakunan kajarawa a lokacin yunkurin Mashrudia, ya kuma bada fatawar yakar turawa yan mulkin mallaka wadanda suke son mamayar kasar Iraqi bayan yakin duniya na daya. Sannan ya je fagen fama da kamsa. Har ila yau bayansa dansa Aya. Sayyed Abulkasim Kashani yana daga cikin malaman da suka goyi bayan Priminista Dr Mohammad Musaddiq wajen maida ikon gwamnatin Iran kan arzikin man fetur da All...ya huwace mata.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 76 da suka gabata a rana irin ta yau wato 14-Yuni-1940M. Sojojin NAZI na kasar Jamusa sun mamaye birnin Paris na kasar Faransa a yakin duniya na biyu. Kafin haka dai a ranar 5-Yuni na wancan shekara ne shugaba Hitla na kasar Jamus ya bada umurni mamayar kasar Faransa, a cikin yan kwanaki sojojinsa sun sami nasarar shiga kasar ta Faransa. Sai kuma a ranar 10 ga watan yuni shugaban Museleni na kasar Ialia wanda yake bangaren kasar Jamus ya shelanta yaki kan kasashen faransa da Britania. Don haka sojojin faransa sun shiga yaki da kashe biyu a cikin kwanaki goma. Da haka aka fi Karfin sojjin Faransa, sojojin Jamus suka shiga birnin Paris a rana irin ta yau ba tare da wata turjiya ba.