Jun 12, 2016 08:45 UTC

Yau Alhamis 26-Khurdod-1395H.SH= 09-Ramadan-1437H.K.=15-Yuni-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 308 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Yuni-1708M.  Turawan Ingila a kasar Britania sun murkushe burin mutanen yankin Scortlanda daga arewacin kasar na neman 'yencin kai daga Ingial. Turawan ingila sun dade suna son hada yankin scotlanda da kasarsu, amma hakan bata samu ba sai bayan da Sarki James I ya zama sarkin Scotlanda da Ingila a shekara ta 1603M, sai dai a gaskiyan lamarin turawan Ingila ne suke iko da kasashen biyu. Wannan halin ya ci gaba har zuwa shekara ta 1707M a lokacinda aka hade majalisun kasashen biyu, wanda ya ingiza mutanen Scotlanda suka yi bore a shekarar da ta biyu, amma sojojin ingila suka murkushe boren da karfi a rana irin ta yau. Amma mutanen yankin scotlanda basu daddara ba suna ta neman 'yencin yankin daga kasar Ingila ta hanyoyi daban daban na baya bayan nan shi ne wanda suka tialstawa ingila amincewa da kafa majalisar yankin a shekara 1999M.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 15 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Yuni-2001M. Aka kafa kungiyar ta kasashen Asia ta tsakiya mai suna Shangai wadanda suka hada da Rasha, China, Qazakistan, Qirqizistan, Tajakistan da kuma  Uzbekistan. Manufar kafa kungiyar dai ita ce bunkasa harkokin tattalin arziki siyasa da kuma tsaro a tsakanin kasashen. Kafin haka dai kasashen biyar ne, banda Uzbekistan suka fara kafa kungiya mai suna (Shangai 5) a shekara 1996 bayan wagajewar tarayyar Soviet. A halin yanzu dai kasashen Iran, Pakistan, Afganistan da Mongolia sun shiga kungiyar ta Shangai a matsayin masu sanya ido. Kungiyar shangai ita ce kungiya mafi girma a yankin Asia a fagen tattalin arziki yawan mutane da kuma karfin soje.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 9 da suka gabata a rana irin ta yau wato 26-Khurdod-1386H.SH. Ayahil- Uzama Mohammad Fadle Lankarani daya daga cikin manya manyan maraji'ai a nan Iran ya rasu. An haifi Aya. Lankarani a shekara ta 1310H.SH a birnin Qum. Ya fara karatu tun yana matashi sannan ya kammala karatu a gaban manya manyan malamai na lokacin wadanda suka hada da Aya. Burujadi da Kuma Imam Khomaini (q). Aya. Lankarani yana tare da malaminsa imam Khomani (q) a yankurin da ya fara a shekara 1342H.SH. don haka ne ma jami'an sarki sha sun sha daure shi, ko korarshi daga Qum. Bayan samun nasarar juyin musulunci a shekara ta 1357H.SH ya ci gaba da goyon bayan JMI ya kuma ci gaba da tarbiyantar da Dalibai har zuwa rasuwarsa a rana irin ta yau.