Jun 12, 2016 08:57 UTC
  • Ko Kun san na (89) 27 Khurdod Shekara Ta 1395 Hijira Shamsia

Yau Alhamis 27-Khurdod-1395H.SH= 10-Ramadan-1437H.K.=16-Yuni-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1440 da suka gabata a rana irin ta yau wato 10-Ramadan-Shekara ta 3 kafin hijira daga Makka zuwa madina. Ummul Muminia Khadija 'yar Khuwaila matar manzon All..(s) ta farko ta Rasu a Makka. Kafin haka dai ta kasance cikin mata masu daraja da daukaka a Makka, sannan ta auri manzon Al..(s) shekaru 15 kafin manzancinsa. Sanna ita ce ta fara karban kiransa. Ta kuma bada duk abinda ta mallaka na duniya don daukaka addinin All...ta'ala. Manzon All..(s) yakan kira shekarar rasuwarta da kuma Amminsa Abutalib a matsayin shekarar bakin ciki. Khadija (s) tana da matsayi a wajen manzon Al..(s) wanda ya sa a suk lokacinda ya tunata sai ya ambato alkheranta. A wani wuria yana cewa " Na rantse da Al... All.. bai bani mata fiye da khadiza ba, ta yi imani da ni a lokacinda aka kafirce mani, ta bani dukiyanta a lokacinda kowa ya haramta mani duniyarsa sannan ta gasgatani a lokacinda kowa ya karyata ni.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Khurdod-1358H.SH. Imam Khomaini (q) wanda ya assasa JMI ya bada umurnin kafa hukumar "Jihadin gina kasa" a Iran da nufin kyautata rayuwar mutanen kasar musamman mutanen karkara a bangaren tattalin arziki. Hukumar jihadin gina kasa ta sami mutane masu ilmi daga dukan bangarori wadanda suka bada gudumawarsu wajen aikin gina kasa, wadanda suka hada da gida madatsun ruwa,  masana'antun a yankunan karkara, bunkasa ayyukan noma da kiwo da sauran bangarori masu yawa. Bayan shekara da kafa wannan hukumar rayuwar mutanen kasar Iran musammana a karkara sun kyautatu sosai. Amma  a shekara 1362 H.SH an maida hukumar a matsayin ma'aikata. Sannan a shekara ta 1379H.SH an hade ta da ma'aikatar noma da kiwo.

03- Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 34 da suka gabata a rana irin ta yau wato 27-Khurdod-1361H.SH. Aka kafa Jami'ar "Ozoz Islami" a nan Kasar Iran. Jami'ar ta fara da dalibai 3000 wadanda aka dauko daga yankuna daban daban na kasar. A halin aynzu jami'ar "Ozoz Islamia" tana da rassa a wasu kashe 10 a duniya. A shekara ta 2012 hukumar fayyace matsayin jami'oi a duniya URAP ta sanya jami'ar Ozo Islamia a matsayin na 226 a duniya, sannan na biyu a cikin Iran, bayan jami'an Tehran. A halin yanzu dai jami'ar tana da dalibai kimani 1,700,000 a cibiya da kuma rassanta.