Jun 15, 2016 07:26 UTC

Yau Jumma’a 28- Khurdod-1395H.Sh =11-Ramadan=1437H.K.=17-Yuni-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 584 da suka gabata a rana irin ta yau wato 11-Ramadan-853H.K. Sheikh Ibrahim Karaki masanin adabin larabci da kuma hadisi ya rasu a birnin Alkahira na kasar Masar. Bayan kamala karatun sharer fage Sheikh Karaki ya je manya manyan makarantu a cikin kasar Masar inda ya kamala karatu a gaban manya manyan malamai na zamaninsa. Daga karshe Sheik Karaki ya zama babban malami a fannin Adabin Larabci Hadisi da kuma tafsirin Alqur’ani mai girama. Littafin «اعراب المفصل» na daga cikin rubuce rubucen Sheikh Ibrahim a cikin fannin ilmin qur’ani.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 219 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Khurdod-1176H.SH. Ogo Mohammad Khan Qajar Sarki na farko daga cikin sarakunan dangin Qajarawa yam utu a yankin Gorgistan. Mohammad Khan ne ya kawo karshen sarautar dangin Zandiyye da karfin takobi, inda ya zubar da jinin mutane da dama kafin ya kai ga iko da kasar Iran gaba dayanta. Daga karshe a shekara ta 1174 ya sanyawa kansa kamben sarauta a birnin Tehran a wancan shekara. Sai kuma bayan shekaru biyu ya jagorancin wata rundunar sojoji zuwa yankin Kafkas inda a nan ne masu gadinsa su biyu suka halaka shi yana dan shekara 63 a duniay. Sarki Muhammad Khan bai da da, don haka ne aka nada dan dan uwansa Fat-Ali sha a kan kujerar sarautar kasar Iran.

03- Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 37 da suka gabata a rana irin ta yau wato 28-Khurdod-1358H.SH. SayyeedAhmad Khusroo-Shahi daya daga cikin manya manyan malamai masu gwagwarmaya a nan Iran ya rasu. An haife shi a garin Tabriz a shekara ta 1314H.SH bayan kamala karatun sharara fage, da shi da mahaifinsa sun yi gudun hijira daga garin Tabriz don takurawan sarki Mohammad Pahlawi sanadiyyar nuna rashin amincewarsu da hana mata sanya hijabi a kasar da yayi. Sayyeed Khusroo ya koma birnin Mashad inda ya kamala karatunsa ya kuma dawo birnin Qum ya ci gaba da karantarwa.. Sai kuma bayan da Imam Khomaini(q) ya fara yunkurinsa a shekara ta 1342 H.SH Sayyeed Ahmad Khusroo-Shahi yana daga cikin malamai da suka goya masa baya har zuwa nasara.