Jun 15, 2016 07:28 UTC

Yau Asabar 29- Khurdod-1395H.Sh =12-Ramadan=1437H.K.=18-Yuni-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1436 da suka gabata a rana irin ta yau wato 12-Ramadan –Ta farko bayan hijira daga makka zuwa Madina. Bayan hijirar manzon All…(s) daga maka zuwa madina ya kulla yanuwantaka tsakanin sahabbansa wadanda suka yi hijira da shi zuwa Madina da kuma sahabbansa na garin madina. A lokacinne manzon All..(s) ya kulla yan uwantaka tsakanin kansa da Aliyu dan Abi Talib (a) inda yace kai dan uwanane a duniya da lahira. Wannan matakin da manzon All.. (s) ya dauka dai ya taimaka wajen cire kabilanci da sonkai tsakanin musulmi, inda ya maida su daya ya kuma hada kansu. Wannan halin ya ci gaba zuwa wani lokaci wanda All… ya kawo karshensa.

02-Masu sauraroko kun san cewashekaru 39 da suka gabata a rana irin ta yau wato 29-Khurdod-1356H.SH Dr Ali Shari’ati daya daga cikin malaman zamani masu gwagwarmaya da sarakunan Pahalawi ya rasu . An haifi Dr Shari’ati a kusa da garin sabziwar a arewacin kasar Iran ya kamala karatunsa na Jami’a a nan birnin Tehran. Sannan ya sami darajar doktora a jami’an sarbon na kasar Faransa. Dr Ali Shari’ati da Malaman addini wadanda suka hada da Shaheed Mutahhari da Dr Bohunar sun raya Husainiyya ershad a nan birnin Tehran. Inda husainiyar ta zama cibiyar yada addinin musulunci a mahangar malaman zamani da kuma malaman hauza ga matasan kasar Iran. Dr Shari’ati ya rubuta littafai sun kai 200 masu muhiammanci daga cikinsu sun hada da «اسلام و انسان»، «تاریخ تمدن»، »، «حج» و «فاطمه، فاطمه است..

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 19 da suka gabata a rana irin ta yau wato 18-Yuni-1997M. Tare da takurawar sojojin kasar Turkia wanda basa kaunar ganin masu kishin addini rike da iko a kasar Priministan kasar Turkia na lokacin mai kishin addinin Najmooddeen Erbakan ya sauka daga kan mukaminsa. Kafin haka dai jam’iyyarsa ta Rafa ta sami rinjaye a majalisar dokokin kasar, da haka kuma ya zama Priminista. Amma don ra’ayinsa na kauracewa HKI da kuma karfafa dangantaka da kasashen musulmi ya sa Majalisar koli ta tsaron kasar Turkiia wacce sojojin kasar wadanda ba ruwansu da addini suke da iko a kanta ya tilastawa Erbakan sauka daga mukamin Priminista. Ta kuma haramta masashiga harkokin siyasa na tsawon shekaru 5 sannan ta haramta jam’iyyarsa ta Rafa a kasar. Erbakan ya rasu a cikin watan Febrerun shekara 2011M.