Ko kun san na (92) 30 ga watan Khurdod shekara ta 1395H.SH.
Yau Lahadi 30- Khurdod-1395H.Sh =13-Ramadan=1437H.K.=19-Yuni-2016M
01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1342 da suka gabata a rana irin ta yau wato 13-Ramadan-95H.K. Hajjag bin Yusuf Athaqafi walin garin Kufa a zamanin sarakunan bani umayya ya halaka. Hajjaj ya shahara da kekacewar zuciya da kuma zubar da jinin makiyansa musamman yan shia. Malaman taruhi sun bayyana cewa Hajjaj bin Yusuf ya kasha mutane kimani dubu 120 a zamanin sarki Abadul malik bin Marwan da kuma dansa Hasham dan Abdul malik. Banda haka Hajjaj ya rusa dakin Kaaba a shekara ta 74 hijira kamariyya sai kuma a karshen rayuwarsa ya haukace. Da ya halaka kuma an bisne gawarsa a boye don kada makiyansa sun dauki fansa a kan gawar tasa.
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 14 da suka gabata a rana irin ta yau wato 30-Khurdod-1381H.SH. Munafukai makiya JMI sun tada bom a cikin haramin Imam Riza (q) limami na 8 daga cikin lamamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s) a ranar Ashoora ba wancan shekara. Sun dada bom din ne a lokacinda masoya iyalan gidan manzon Al…(s) sukayi cinkoso a cikin haramin suna makokin shahadar Imam Husain (a) . Mutane da dama ne suka yi shahada sanadiyar tashin bon din wasu kuma suka ji raini. Jagoran juyin juya halin musulunci Aya. Sayyeed Aliyul Khaminaee ya yi jawabi bayan tashin bom din inda y ace su munafikai sun bayyana cikekken faskarsu na rashin mutunta duk abinda mutanen kasar Iran suke mutuntawa, sanna adawarsu da mutanen kasar Iran bata san iyaka ba .
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 14 da suka gabata a rana irin ta yau wato 30-Khurdod-1381H.SH. Allamah Sayyeed Saeed Akhtar Razawi malamin addinin na mazhabar iyalan gidan manzon All..(s) ya rasu a birnin Darassalam na kasar Tanzania.
An haifi sayyeed Akhtar a shekara ta 1305H,SH a kasar India a can ya kamala karatunsa na addini. Sanna yana dan shekara 35 a duniya yak aura zuwa kasar Tanzania daga gabacin Afrika inda ya fara yada mazhabar shia a can. Kafin rasuwarsa mahabar ta yadu a cikin kasar da kuma kasashen da dama a yakin sanadiyyar ayyukansa. A cikin ayyukan allama Akhtar dai akwai, gina makarantu tarjamar littafai cikin harsuna na turanci da Kiswahili da sauransu. Bayan shekara kimani 43 na tabligi a kasar Tanzania allama Akhtar ya rasu a rana irin ta yau a birnindarussalam yana dan shekara 76 a duniya.