Aug 16, 2016 04:45 UTC

Yau Jumma'a 29-Murdod-1395H.SH=16-Zulkida-1437H.K.=19-Augusta-2016M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 28 da suka gabata a rana irin ta yau wato  29-Murdod-1368H.SH. Gwamnatin kasar Amurka ta amince da kuskuren sojojinta na ruwa wadanda suka cilla makaman linzami kan jirgin fasinja Iran air dauke da fasinjoji daga birnin Bandar Abbas zuwa Dubai. A rana 12-Teer-1367H.SH ne sojojin Amurka da suke cikin Tekun farisa suka cilla makaman linazami kan jirgin fasinjar dauke da Fasinjiji 298, daga cikinsi akwai yara yan kasa da shekaru 13, su 66, mata 53 da kuma wasu yan kasashen waje 46, duk suka mutu. Amma sai bayan kwanaki 45 gwamnatin Amurka ta bayyana cewa kuskure ne daga sojojinta na ruwa. Duk da cewa da wuya ya zama hakan , tunda akwai bambanci tsakanin jirgin fasinja da na yaki. Banda haka gwamnatin Amurkan ta bawa komandan sojin ruwan da suka yi wannan aiki lambara kasa ta girmamawa.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 25 da suka gabata a rana irin ta yau wato 19-Augusta-1991M. Wasu manya manyan sojojin kasar tarayyar Soviet na lokacin karkashin jagorancin Ganadi Yonoyuf sun yi yunkurin juyin mulki wa shugaban tarayyar Soviet na karshe wato Mechiel Gurbachef, don dakatar da sauye sauyen da yake gabatarwa a harkokin siyasar tarayyar ta Soviet da kuma hada tarayyar Rushewa. A lokacin juyin mulkin dai Gorbachef yana hutu a tsibirin Cramia a arewacin tekun black sea. Shugaban tarayyar Rasha na lokacin Boris Yeltson ne ya yi yunkuri na hana juyin mulkin samun nasara. Don haka bayan kokarin juyin mulkin Yalsen ya shahara don haka bayan wargajewar tarayyar soviet a karshen shekara ya zama shugaban tarayyar Rasha na farko.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 9 da suka gabata a rana irin ta yau wato 29-Murdod-1386H.SH. Aya. Uzma Mohammad Husain Bahajati Yazdi, babba malamin addinin mai gwagwarmaya ya rasu. An hafi Aya. Yazdi a shekara ta 1314H.SH a garin Urdukan kusa da birnin Yazda. Ya fara karatu a yana dan shekara 7 a duniya daga nan ya je birnin Qum da zama inda ya zama abokan karatu na Aya. Mas'udi Khumaini, Hashin Rafsa jani da kuma jagoran juyin juya halin muslunci na Iran a yanzu. Bayan kammala karatu kasance tare da Imam khomani (q) a duk tsawon gwagwarmayanshi da sarakunan Iran. Bayan nasarar juyin musulunci Imam ya nada shii limamain masallacin Yaz. Aya yaz ya rasu yana dan shekara 73 a duniya a shekara 1386H.SH.