Ko Kun San Na (154) 30 Ga Watan Murdod-1395 Hijira Shamshia
Yau Asabar 30-Murdod-1395H.SH=17-Zulkida-1437H.K.=20-Augusta-2016M.
01-Masu sauraro ko kun san cewa yau ce 30 ga watan Murdod ranar girmama Allamah Baqir Majlisi babban malami dan kasar Iran wanda ya rubuta littafin Biharul-anwar wanda yawansa ya kai mujalladai 110. Allama Majlisi ya fara karatu tun yana dan shekara 4 a gaban mahaifinsa Mohammad Taqi Majalisi. Don irin baiwar da Al.. ya yi masa na fahintar karatu yana dan shekara 14 a duniya malaminsa Sheikh Bahae ya bashi izinin ruwaita hadisai na manzon All.. da Imamai. Allahma Majlisi ya rubuta littafin Beharun Anwar cikin shekaru masu yawa, inda ya tattara hadisai na manzon All…(s) da kuma iyalan gidansa. Banda haka yana da wasu litafai wadanda suka hada da
حقُّ الیقین، ، مشکوةُ شرح اربعین حدیث ، مِراةُ العُقول و رسالةٌ فی الاوزان
02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1258 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Zulkida-179H.K. Sarki haruna Rasheed daya daga cikinn azzalumaisarakunan Abbsiyawa ya tilastawa Imam Musal-Kazim (q)mlimami na 7 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s). daga Madina zuwa bagdaza mazauninn cibiyar abbasiyawa. Da farko ya zauna a kurkukkun Isa Bin jaafar, daga baya Isa yace ba zai iya ci gaba da tsare shi ba. Sai kuma ya maidoge bagza. Daga karshe bayan ya zauna shekaru 15 a gidan tari yahya barmaki daya daga cikin waziran Haruna ya bada Umurnin kaishi ga shahda.
03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 124 da suka gabata a rana irin ta yau wato 17-Murdod-1313H.SH. wani matashi mai suna Amir Riza Kirmani ya kashe sarki daga saraki Nasirudddeen Qajar daya daga cikin nsarakunan Qajarawa a nan Iran. Bayan mutuwar mahaifinsa Sarki Mohammad Sha, ya gaji mahaifinsa kan kujerar a shugabancin kasar Iran yana dan shekara 16 a duniya Sannan yayi shekaru 50 yana mulki, shi a rana irin ta yau ya je haramin abdulazeem alhasi sai aka kashe shi yana dan shekara 66 a duniya. Bayan mutuwarsa dansa Zafaruddeen shad an shekara 45 wanda yake rikeda matsayin yerima mai jiran gadona shekara 40.