Libya: Kashe Mutane 4 A yankin Banighazi Saboda Tashin Nakiya
Aug 24, 2016 07:52 UTC
Wata Nakiya da ta tarwatse a garin Banighazi da ke gabacin kasar Libya, ta kashe mutane 4.
Wata Nakiya da ta tarwatse a garin Banighazi da ke gabacin kasar Libya, ta kashe mutane 4.
Mazauna yankin Qurashe da ke yammacin birnin Banighazi sun ce, bayan tashin nakiyar, an ci gaba da fada a tsakanin sojojin gwamnati da kuma kungiyoyin da su ke dauke da makamai a yankin.
Tsoma bakin kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato a cikin kasar Libya wanda ya kai ga kashe tsohon shugaban kasar Mua''ar Khaddafi a 2011, ya share fagen tabarbarewar harkoki tsaro a kasar ta Libya.
Tags