Kamaru / Boko Haram : An Yankewa Mutane 109 Hukuncin Kisa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10179-kamaru_boko_haram_an_yankewa_mutane_109_hukuncin_kisa
Wata kotun soji a birnin Maroua dake Kamaru, ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutane 109 bisa samunsu da hannu a ayyukan ta'adanci dake da alaka da kungiyar boko haram.
(last modified 2018-08-22T11:28:49+00:00 )
Aug 26, 2016 13:57 UTC
  • Kamaru / Boko Haram : An Yankewa Mutane 109 Hukuncin Kisa

Wata kotun soji a birnin Maroua dake Kamaru, ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutane 109 bisa samunsu da hannu a ayyukan ta'adanci dake da alaka da kungiyar boko haram.

Bayanai daga kasar sun nuna cewa sama da mutane 1,000 ke tsare a gidajen yari daban daban na kasar bisa zargin hada kai da kungiyar 'yan ta'ada ta boko haram.

Saidai a cewar labarin, bisa ga dukkan alamu wannan hukuncin zai ci karo da kungiyoyin dake yaki da irin wannan hukuncin a wannan kasa irinsu (RACOPEM) data kunshi lauyoyi.

Wannan dai ba shi ne karo farko ba da ake yanke hukuncin irin wannan a Kamaru, inda ko a watan Maris na wannan shekara kotun soji ta Maroua ta zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutane 89 da ta samesu da laifin kai hare-hare ko kuma bayar da hadin kai ga kungiyar Boko Haram.

Kamaru dai na gada cikin kasashen da suke fuskantar hare haren ta'adanci masu nasaba da kungiyar boko haram, na baya bayan nan dai shi ne wanda yayi sanadin mutuwar mutane akalla hudu a gundumar Mora dake yankin arewa mai nisa.