Mummunan Hali A Birnin Banighazi Na Kasar Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1018-mummunan_hali_a_birnin_banighazi_na_kasar_libya
Birnin Banighazi Na fama Da Karancin Abinci Da Magani
(last modified 2018-08-22T06:57:50+00:00 )
Feb 20, 2016 05:59 UTC
  • Mummunan Hali A Birnin Banighazi Na Kasar Libya

Birnin Banighazi Na fama Da Karancin Abinci Da Magani

Magajin garin birnin Banigazi da ke gabacin kasar Libya, ya bayyana cewa suna fama da matsaloli masu yawan gaske.

Umar Muhammad al-Burasy ya ci gaba da cewa; mutanen na Banighazai suna fuskantar matsaloli da su ka kunshi karancin abinci da magani.

Har ila yau, magajin garin na Banighazi ya ce; A kowace rana ta Allah 'yan ta'addar suna harba makamai masu linzami akan yankuna daban-daban na yankin, kuma suna kai hare-hare akan asibitoci da makarantu da sauran cibiyoyin da ba na soja ba.

Umar Muhammad al-Burasy ya kuma yi suka da kayakkausar murya akan kungiyoyin kasa da kasa da su ke yin shiru akan abinda ya ke faruwa a kasar ta Libya ba tare da sun aimaka ba.