MDD Ta Aike Da Taimakon Abinci Ga 'Yan Gudun Hijirar Chadi
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa ta aike da kayayyakin abinci ga dubban 'yan gudun hijirar kasar Chadi da rikicin kungiyar Boko Haram ya tarwatsa su.
A wata sanarwa da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a jiya Juma'a ta bayyana cewa a kokarin da ake yi na rage wa dubban 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba su da gidajensu, majalisar ta aike da abinci ga kimanin 'yan gudun hijira dubu biyar a garin Baga Sola da ke arewacin Tafkin Chadi.
Sanarwar ta kara da cewa MDD tana ci gaba da neman hanyoyin da za ta isar wa kimanin 'yan gudun hijira dubu 35 da ke bukatar abinci na gaggawa da abincin da suke bukata kafin karshen wannan watan.
Rahotanni sun bayyana cewar sama da mutane dubu 100 ne suka rasa gidajensu a yankin sakamakon hare-haren kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram.