Dakarun tsaron Libiya sun killice mayakan kungiyar ISIS A birnin Syrte
Dakarun tsaron Libiya sun samu nasarar killice mayakan kungiyar ISIS A birnin Syrte
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa Dakarun tsaro masu biyayya da Gwamnatin hadin kan kasar Libiya sun samu nasarar killace mayakan ISIS a garin Syrte a yau Litinin. kuma a halin da ake ciki wasu daga cikin Dakarun tsaron sun kuza cikin garin, suna ci gaba da kwabza fada da mayakan na ISIS .
A tsakiyar shekarar 2015 din da ta gabata ce mayakan na ISIS suka mamaye garin Syrte ma'aifar tsohon shugaban kasar Marigayyi Kanal Mu'amar Kaddafi, lamarin da ya janyo tsoro da fargaba a zukatan Al'ummar garin.
Farmakin kwato garin na Syrte dake a matsayin babbar tungar mayakan kungiyar ISIS din a arewacin Amurka, an fara shi kimanin watanni uku da suka gabata kuma ana san ran nan da 'yan kwanaki za a kwace shi daga hanun mayakan na ISIS.
Majiyar Asibitin kasar ta ce akalla Sojojin Gwamnati 34 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 85 na daban suka jikkata a yayin farmakin karshe da Sojojin kasar suka fara na kwato garin Syrte din a jiya Lahadi.