Za'a Gudanar Da Taron Tattalin Arzikin Kasashen Afirka A Kasar Masar
A yau Asabar ne za a bude wani taron tattalin arziki na wasu shugabannin kasashen Afrika da gwamnatin kasar Masar ta shirya gudanawar da za a gudanar da shi a wajen shakatawar nan na Sharm-el-Sheikh da ke kasar.
A wata sanarwa da gwamnatin kasar Masar din ta fitar ta ce shugaban kasar, Abdel Fatah Al-Sisi shi ne zai bude taron da jawabin da zai gabatar inda zai yi bayanin kan manufar taro da kuma hanyoyin da za a bi wajen cimma manufofin taron na fadada alaka ta kasuwanci a tsakanin kasashen Afirkan da kuma na duniya.
Har ila yau sanarwar da aka buga a shafin internet na taron ta ce daga cikin shugabannin da za su yi jawabi a wajen taron sun hada da shugaba Nijeriya Muhammadu Buhari da takworinsa na kasashen Kenya Uhuru Kenya da Sudan Umar al-Bashir da Togo Faure Gnassinbe da Gabon Ali Bango da sauransu, bugu da kari kan wasu hamshakan 'yan kasuwa na nahiyar Afirka ciki kuwa har da Alh. Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa kudi a Afirkan.
Taron dai na kwanaki biyu zai mayar da hankali wajen karfafa huldar kasuwanci tsakanin kasashen Afrika da sauran takwarorinsu na duniya.