Libya : Dakarun Gwamantin Hadaka Sun Doshi Yankunan karshe Da (IS) Ke Rikeda
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10363-libya_dakarun_gwamantin_hadaka_sun_doshi_yankunan_karshe_da_(is)_ke_rikeda
Gwamnatin hadaka ta Libiya ta sanar da cewa dakarunta sun doshi yankunan karshe da 'yan ta'adda na (IS) ke rikeda a birnin Syrte.
(last modified 2018-08-22T06:58:51+00:00 )
Aug 30, 2016 12:12 UTC
  • Libya : Dakarun Gwamantin Hadaka Sun Doshi Yankunan karshe Da (IS) Ke Rikeda

Gwamnatin hadaka ta Libiya ta sanar da cewa dakarunta sun doshi yankunan karshe da 'yan ta'adda na (IS) ke rikeda a birnin Syrte.

Wat5a sanarwa da gwamnatin ta wallafa a shafinta na facebook ta ce dakarun sun kutsa kai a yankin wanda shi ne na karshe inda 'yan ta'addan sukayi kaka-gida.

dama kafin hakan gwamnatin ta sanar da korar 'yan ta'addan kwata-kwata daga unguwar N1, dake cikin wurare da 'yan ta'addan ke rikeda a birnin na Syrte bayan mumunan fadan da aka gwabza.

A ranar Lahadi data wuce ne dakarun gwamnatin hadaka na Libya suka shiga gadan-gadan yaki kwato daukacin ikon birnin na Syrte dake a yankin gabar tekun bahar rum a kilomita 450 daga gabashin Tripoli. 

kimanin dakarun gwamnatin 50 suka ras arayukan su kana wasu 200 suka jikkata a fadan da aka kwashe ranakun Litinin da lahadi anayi a cewar wasu majiyoyin asibiti.