Wakilan MDD sun gana da magabatan Gwamnatin Aljeriya kan rikicin Libiya
Wakilin MDD na musaman kan kasar Libiya ya gana da jami'an Ma'aikatar harakokin wajen Aljeriya kan rikicin Libiya
Kamfanin dillancin Labaran Xin Huwa na kasar China ya habarta cewa A jiya Assabar manzon Majalisar dinkin Duniya na musaman kan kasar Libiya Martin Kobler ya gana da Abdelkader Messahel babban Jami'i a Ma'aikatar harakokin wajen Aljeriya a birnin Alje fadar milkin kasar Aljeriya, inda suka tattauna kan barazanar da yankin ke fuskanta sanadiyar samuwar 'yan ta'addar IS a Libiya.
A yayin ganarwar Mista Kobler ya bayyana muhimiyar rawar da kasar Aljeriya ke takawa wajen tabbatar da sulhu a Libiya sannan ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za tsarkake garin Sirte daga hanun kungiyar IS.
Har ila yau Mista Kobler ya sanar da cewa nan da 'yan kwanaki masu zuwa za a gudanar da sabuwar tattaunawa sulhu kan kasar Libiya a birnin Tunus na kasar Tunusiya.
A nasa Bangare, Abdelkader Messahel ya ce wajibi ne kungiyoyin kasa da kasa su kara himma wajen tabbatar da sulhu gami da konciyar hankali a kasar ta Libiya.