Sojojin Kasar Yemen Sun Kashe Sojojin Saudia Da Hadaddiyar Daular Larabawa Hudu
Sojojin kasar Yemen tare da tallafin mayakan sa kai sun kashe sojojin kasar Saudia biyu a kudu masu yammacin kasar da kuma na kasar hadaddiyar daular larabwa gudu.
Majiyar shafin yanar gizo na almasira ya nakalto cewa sojojin kasar Yemen kwararru a harbi sun kashe sojojin saudia da na amerate su hudu a maida martani ga hare haren da suke kaiwa kan kasarsu.
Majiyar labarai na kasar saudia sun tabbatar da wannan labarin sun kuma bada sunayen mutanen da aka kashe sun hada da Lieutenant Mohammed al-Bhijan and Sergeant Ali al-Asiri. Har'ila yau soja na ukku shi ne Waze’ al-Dilafe wanda aka kashe a yankin Asir na kasar ta Yemen.
A wani bangare kuma kamfanin dillancin labaran kasar Emerate ya bada sanarwan cewa an kashe sojan kasar guda a kasar Yemen.