Fara Kaddamar Da Babban Farmaki 'Yan Ta'adda A Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1066-fara_kaddamar_da_babban_farmaki_'yan_ta'adda_a_libiya
Dakarun tsaron Libiya sun fara kai wani babbar farmaki na kakkabe 'yan ta'adda a Birnin Bangazi
(last modified 2018-08-22T06:57:50+00:00 )
Feb 21, 2016 03:04 UTC
  • Fara Kaddamar Da Babban Farmaki 'Yan Ta'adda A Libiya

Dakarun tsaron Libiya sun fara kai wani babbar farmaki na kakkabe 'yan ta'adda a Birnin Bangazi

Jaridar Alyaumu Sabi'i ta kasar Masar ta nakalto wata majiyar tsaron kasar Libiya na cewa a jiya Assabar Dakarun tsaron kasar sun fara kai farmaki kan sansanin'yan ta'addar na birnin Bangazi dake arewa maso gabashin kasar

farmakin da aka bashi sunan jinin shahidai ya fara samun ci gaba a anguwanin Laisi da Bawa'atini.

A bangare guda Ma'aikatar dake kula da hulda ta Dakarun tsaron kasar ta sanar da cewa wannan farmaki na gudana ne kalkashin jagorancin Khalifa Haftar babban hafsan sojojin kasar kuma tun bayan fara wannan aiki janar Haftar ya shagalto da shiryar da Dakarun daga sansanin Sojojin Banina.

Har ila yau Sanarwa ta kara da cewa janar Haftar zai kasance cikin saduwa da dukkanin kwamondojin kasar domin bayar da shawarwari tare bin diddigin yakke farmakin ke gudana.