Wata Mota shake da Bama-bamai ta tarwatse a birnin Tripoli
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10765-wata_mota_shake_da_bama_bamai_ta_tarwatse_a_birnin_tripoli
Majiyar tsaron Libiya ta sanar da tarwatsewar wata Mota shake da Bama-bamai a kusa da Ma'aikatar harakokin wajen kasar dake birnin Tripoli.
(last modified 2018-08-22T06:58:54+00:00 )
Sep 08, 2016 06:20 UTC
  • Wata Mota shake da Bama-bamai ta tarwatse a birnin Tripoli

Majiyar tsaron Libiya ta sanar da tarwatsewar wata Mota shake da Bama-bamai a kusa da Ma'aikatar harakokin wajen kasar dake birnin Tripoli.

Kamfanin dillancin Labaran Reuteus ya nakalto majiyar tsaron Libiya na cewa, tashin bom din ada aka makile a wata Mota ya faru ne a wannan Alkhamis a kan babbar hanyar dake isa zuwa Ma'aikatar harakokin wajen kasar dake tsakiyar birnin Tripoli.

Rahoton ya ce a halin da ake ciki, Jami'an tsaro da na 'yan kwana kwana na iya kokarin su wajen gano wadanda harin ya ritsa da su da kuma irin asarar da ya janyo.

Ya zuwa yanzu dai babu wani cikekken bayyani da aka sanar dangane da wannan hari.