Shugaba Museveni Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Uganda
(last modified Sun, 21 Feb 2016 10:46:54 GMT )
Feb 21, 2016 10:46 UTC
  • Shugaba Museveni Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Uganda

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar, lamarin da ya ba shi damar ci gaba da mulkin kasar zuwa shekaru biyar masu zuwa bayan da ya shafe shekaru 30 yana mulkin kasar.

Rahotanni sun ce shugaba Museveni, dan shekaru shekaru 71 a duniya ya sami kashi 60.75% na yawan kuri'u da aka kada alhali babban mai hamayyar Kizza Besigye, dan shekaru 59 a duniya ya samu kashi 35% na kuri'un da aka kada din.

Sai dai madugun ‘yan adawa Kizza Besigye, wanda kuma karo na hudu kenan yake takarar shugabanicin kasar, cikin wani sako da ya fitar daga inda ake tsare shi, ya bayyana rashin amincewarsa da sakamakon zaben wanda ya ce an tafka magudi inda ya kirayi magoya bayansa da kada su amince da sakamakon zaben.

Masu sanya ido daga kasashen Turai dai sun bayyana damuwarsu dangane da abin da suka kira siyasar barazana da kuma razana 'yan adawa da gwamnatin kasar ta dauka lamarin da ke sanya alamun tambaya kan ingancin zaben.