Shugabannin Afirka Sun Cimma Yarjejeniya Bunkasa Tattalin Arziki A Taron Masar
(last modified Sun, 21 Feb 2016 10:47:44 GMT )
Feb 21, 2016 10:47 UTC
  • Shugabannin Afirka Sun Cimma Yarjejeniya Bunkasa Tattalin Arziki A Taron Masar

Shugabannin Afirka bugu da kari kan wasu gungun 'yan kasuwa sun cimma matsaya kan shirin da suke da shi na karfafa tattalin arziki da zuba jari a nahiyar duk kuwa da barazanar da ta'addanci da nahiyar yake fuskanta.

Shugabannin na Afirka sun cimma hakan ne a taron karfafa huldar kasuwanci tsakanin kasashen Afirka na kwanaki biyu da aka bude a jiya Asabar a wajen shakatawar nan na Sharm el-Sheikh na kasar Masar don karfafa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin wasu kasashen Afirkan su 26 da nufin samar da kasuwa guda a nahiyar ta Afirka.

A jawabin bude taron, shugaban kasar Masar kuma mai masaukin baki Abdul Fattah Al-Sisi ya bayyana cewar manufar taron ita ce kokari wajen karfafa kasuwanci da harkar zuba jari a nahiyar Afirkan don karfafa matsayar Afirkan a tattalin arzikin duniya.

Taron dai wanda kasar Masar da kungiyar Tarayyar Afirka suka shirya, ya sami halartar shugabanin kasashen Nijeriya, Sudan, Togo da Gabon da wani adadi mai yawa na ministoci da manyan jami'an gwamnatoci bugu da kari kan 'yan kasuwa.